Shin Ulsa na iya zama ciwon daji? Ga abin da Likitoci ke cewa

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments
Aproko Doctor a kan ciwon daji

Fitaccen likitan nan mai wayar da kan mutane a kafafen sadarwa, Dr. Chinonso Fidelis Egemba ya yi ƙarin haske game da ciwon daji da yadda alamominsa su ke ɓoyewa su zama kamar alamun cutar ulsa.

Tsokacin likitan ya zo ne a daidai lokacin da fitaccen jarumin fina-finan Najeriya, Taiwo Hassan ya rasa ranshi sakamakon ajalin da ciwon daji ya yi masa.

Likitan ya yi bayani cewar mutane su na kuskurewa ciwon daji ta yadda ake mamakin yadda za a ga mutum garau kuma daga baya a ce ya mutu sanadiyyar ciwon daji.

DABO FM ta tattara cewar ya wallafa bayanai masu yawa a shafinshi na X, in da ya yi ƙarin haske tare da sanar da mutane abubuwan da ya kamata su sani game da ciwon dajin.

“Maganar gaskiya, ganin mutum lafiya kalau a fuska ba ya nufin cewar mutum ya na da cikakkiyar lafiya. Wasu manyan cututtukan su na fara wa ne da ƙananun alamu waɗanda aka mayar da su ba komai ba.”

Ya bayar da misali a kan ulsa.

Ya bayyana cewa duk da dai ciwon ulcer ba ya zama ciwon daji kai tsaye, amma wasu nau’ikan ciwon daji musamman masu kama ciki, su na bayyana ne da alamu irin na ciwon ulsa, wanda hakan ke sa wa mutane su kasa banbance cewar ulsa ce ko kuma ciwon dajin ne, musamman idan ba a je asibiti ba.

Shin ulsa za ta iya zama ciwon daji? Gaskiya ba haka bane kai tsaye. Haka kawai ulsa ba ta zama ciwon daji. Sai dai wasu nau’ikan ciwon daji masu kama ciki su na da alamomin da mu ke gama gari ke kira da alamun ciwon ulsa. Don haka sai mutum ya yi ta yin maganin ulsa amma kuma ciwon daji ne.”

Ya shawarci al’umma cewar idan mutum yana yawan shan maganin ulsa kuma ciwon ya ƙi tafiya, ya sake zuwa a ƙara duba shi, kada ya riƙa siyan magungunan da aka bashi ba tare da ya sake komawa asibiti ba.”

“Kada a yi wasa da alamomi irinsu; ciwon ciki akai-akai, ramewa mara dalili, yawan yin amai, shan wuya wajen haɗiya ko kuma jin ƙoshi idan an ci abincin da bai taka kara ya karya ba. Ba ina cewa waɗanda alamomin ciwon daji bane, amma kada a yi sakaci da su, ya kamata a je asibiti idan ana jin su musamman akai-akai.”

“Ba ina cewa mutum ya tashi hankali don yana jin waɗannan alamomi bane, amma dai kada a zauna ana jinsu har na lokaci mai tsayi ba tare da an je an yi binciken ƙwaƙƙwafi ba.”

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00