Home LabaraiINEC ta bude shafin daukar aiki, ga yadda za ku nema

INEC ta bude shafin daukar aiki, ga yadda za ku nema

by Dabo Online
0 comments

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara buɗe shafin neman aiki daga ‘yan Najeriya a shekarar 2026.

Kamar yadda DABO FM ta gano, hukumar ta buɗe shafin neman aikin a ranar Litinin, 20 ga Yulin 2026, kuma za a rufe shi da tsakar dare na ranar Litinin, 27 ga Yulin 2026.

A cewar INEC, ɗaukar ma’aikatan zai ƙarfafa ayyukan hukumar a fannoni kamar gudanar da zaɓe, rajistar masu kaɗa ƙuri’a, sarrafa bayanai da kuma shirye-shiryen gudanar da zaɓe.

Hukumar ta bayyana cewa ana neman ma’aikata a matakan Grade Level 07, 08, 09, 10 da 12, tare da raba guraben zuwa rukuni daban-daban bisa cancanta da ƙwarewar masu neman aikin.

Daga cikin guraben da aka buɗe akwai na ƙwararru kamar lauyoyi, jami’an fasahar sadarwa (ICT), Injiniyoyi, Akantoci, jami’an lafiya da sauran ƙwararru.

INEC ta jaddada cewa neman aikin ba a biyan ko sisin kobo, kuma tana gargadin masu neman aikin da kada su ba wa kowa kuɗin a yayin neman aikin.

Ga mai bukatar cikewa, zai ziyarci wannan shafin https://recruitment.inecnigeria.org/

Masu sha’awar neman aikin za su buƙaci ƙirƙirar asusu a shafin ɗaukar ma’aikatan INEC, su cike fom ɗin neman aikin tare da loda takardun da ake buƙata kafin wa’adin rufe shafin.

Hukumar ta shawarci duk masu sha’awar aikin da su tabbatar sun kammala rajistarsu kafin ranar 27 ga Yulin 2026, domin ba za a karɓi buƙatun da suka makara ba.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00