Babban Labari Labarai

Covid-19: Ya kamata gwamnati ta kara wadata talakawa da kayayyakin more rayuwa-Abba Adamu Aliyu

A dai-dai lokacin da ake kukan tsadar rayuwa saboda sanya dokar takaita zirga-zirgan a wasu jahohin kasar nan da gwamnatin tarayya ta yi, an bukaci ‘yan kasuwa musamman masu sayar da hatsi da sauran kayan masarufi su yi wa Allah kada su kara farashin kayayyakin masarufi saboda yanayin da aka shiga a kasar nan.

Wani jigo a Jama’iyyar Apc a karamar hukumar Taura da ke Jihar Jigawa Hon Abba Adamu Aliyu ya bayyana hakan sa’ilin zantawar sa da Dabo FM.

Ya kwatanta halin da ake cikin a matsayin wani jarabi daga Allah madaukakin Sarki, ya kuma nuna bakin cikin sa kan yadda wasu ke amfani da wannan lokaci wurin tsawwalawa mabukata da marasa karfi duk da halin kunci da al’umma ke ciki.

Ya kara da cewa, ba yanzu ne karo na farko da ake samun annoba ba, ko zamanin annabawan Allah da sahabbai an samu jarabi ta annoba. Sannan ya yi fatan samo maganin ta nan bada jimawa ba.

Da ya juya ga bangaren gwamnati kuwa, Hon Abba Adamu Aliyu, ya naimi ganin ta wadata al’ummar ta da kayayyakin more rayuwa da zai inganta jin dadin su, sannan ya yaba ma shirin gwamnati na ciyar da mabukata a irin wannan lokaci.

Daga nan sai ya yabawa matakin da gwaman Badaru Abubakar na Jihar Jigawa ya dauka domin magance cutar COVID-19 a Jihar,Kuma ya roki Allah ya zaunar da Najeriya da Jihar Jigawa lafiya.

Karin Labarai

UA-131299779-2