Labarai

Da dumi-dum: Gwamna Zulum ya kulle iyakokin jihar Borno

Ibrahim Mustapha, Maiduguri

Gwamna Babagana Umara Zulum, ya kulle iyakokin fadin jihar Borno batare da matafiya sunshiga jihar ba.

Gwamnan yadauki matakin hakan yunkurin da gwamnatin jihar tace tana yi na dakile cutar Covid-19 duk da bata bulla cikin jihar Borno ba.

DABO FM ta tattaro gwamnan ya bayyana hakane yayin da yake jawabi a gidan talabijin mallakin gwamnatin jihar a yau.

Gwamna yace hakika kulle fadin jihar Borno ba tare da matafiya sun shiga ba itace hanya da zata kai jihar ga tsira daga cutar Coronavirus.

Gwamnan ya kara da cewar dokar tazo da sabon salo bisa karya tsohuwar dokar hana shiga jihar da akayi inda ya bayyana cewar yanzu babu mota da zata shiga ko ta fita daga cikin jihar.

Haka zalika gwamnan ya kara da cewa gwamnatinshi ashirye take don yaki da cutar Covid-19, yace an ware kudi da motoci da wajen kebe masu cutar cikin gaggawa muddin an samu labarin mai dauke da cutar.

Ya kuma shawarci al’ummar jihar da su kasance masu wanke hannayensu da gujewar shiga cikin cinkoso.

Sai dai kuma gwamna yace an amince wa motocin kayan abinci, Mai, Likitoci, motocin agaji su shigo cikin jihar.

Wasu daga cikin al’ummar jihar Borno sun shaidawa Dabo FM, cewa “hakika mu masu mika wuya ne ga gwamna Babagana Umara Zulum.

Karin Labarai

Masu Alaka

Yanzu yanzu: Wadanda Coronavirus ta kama a Najeriya sun zama 111

Dangalan Muhammad Aliyu

Alkaluman ‘Corona Virus’ ya zama 26 bayan sake tabbatar da 4 a safiyar Lahadi

Dangalan Muhammad Aliyu

Mutane 245 sun sake kamuwa da Kwabid-19, 37 a Katsina, 32 a Jigawa, 23 a Kano

Dabo Online

Mu da muke da madafun iko bamaso a fada mana gaskiya – Zulum

Muhammad Isma’il Makama

Yanzu yanzu: An samu karin mutane 22 masu dauke da Coronavirus, jumillar 276 a Najeriya

Dabo Online

Gwamnan jihar Borno bai iske Likita ko 1 ba a ziyarar bazata da ya kai asibitin Gwamnati

Dabo Online
UA-131299779-2