(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');
/

Tankar Mai ta fadi a hanyar Kaduna zuwa Zariya

Karatun minti 1

Da misalin karfe 1 na rana ne wata motar tankar mai da ke shake da man getir ta fadi a kusa da gidan man NNPC a yankin Dan Magaji kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Lamarin da ya faru dab da gadar kwangila Zariya, ya tsayar da zirga-zirgar sufuri a babban hanyar.

Zuwa yanzu hukumar kashe gobara shiyyar Zariya na can sun dukufa wurin kashe wutar da ta tashi.

Wani ganau ya mai suna Malam Usman ya shaidawa manema labarai cewa lokacin da lamarin ya faru an fito da wasu yara a kone da kuma yanzu aka garzaya da su Asibitin Shika domin kula da lafiyar su

Sauran bayanai na tafe

Karin Labarai

Sabbi daga Blog