Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso, Hon Ghali Abdullahi Basaf ya koma sana’ar ɗinki bayan da kotu ta kwace kujerarshi a watannin da su ka gabata.
Yan jami’iyyar NNPP ta yi zargin hakan na da nasaba da rashin nuna goyon bayanshi ga sauya sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jami’iyyar APC.
Da ya ke sanar da komawarshi ɗinki a shafinshi na Facebook, Hon Basaf ya ce bai kamata matasa su mayar da siyasa abar dogaro ita kaɗai ba in da ya ce dole ne matasa su tashi su yi sana’a tuƙuru domin ita ce mai tabbas.
“Yan uwa masu sana’o’in hannu, muna roƙon Allah Ya sanya albarka a sana’o’inmu”
A zantawarshi da Jaridar DailyTrust, Basaf ya ce sana’ar ɗinki ce ta ba shi kuɗin da ya yi amfani da su wajen yin yaƙin neman zaɓen da ya zama shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano.
