/

Hukuncin mutum ya kashe kansa, Daga Sheikh Aminu Daurawa

dakikun karantawa
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Hukuncin mutum ya kashe kansa tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa daga masallacin Ansaru Sunnah da ke karamar hukumar Fagge a birnin jihar Kano.

Huɗubar Juma’a ta yau. 12/ 4/1442. 27/ 11/2020.

Kwanan nan ana ta samun mutane da suke yunkurin kashe kawunan su, bisa wasu dalilai na ƙuncin rayuwa ko rashin samun wata buƙata, ko shiga wata damuwa ko wani matsanancin ciwo ko zazzafan talauci.

Musulunci ya hana mutum ya kashe kansa : “Kada ku kashe kanku lallai allah mai jin ƙaine a gare ku” . Alkur’ani mai girma”.

Hadisai sun zo suna tsoratar da mu bisa hatsarin mutum ya kashe kansa,
Na ɗaya : Hadisin Abu Hurairah, Bukhari da Muslim.

“Duk wanda ya hau dutse ya gangaro domin ya kashe kansa za a kafa masa dutse a wutar jahannama, ya dinka hawa yana gangarowa har abadan abada, duk wanda ya kwankwaɗI guba, ya mutum za a bashi guda a cikin wuta ya yi ta kwankwaɗa har abadan abada, duk wanda ya kashe kansa da wani karfe za a bashi irin wannan karfen a cikin wuta ya yi ta tsakawa kansa a cikin wuta har abadan abada.

Na biyu : Hadisin Jundubi ɗan Abdullahi – Bukhari da Muslim.

Na uku. Hadisin Jabir ɗan Samurata. Muslim ya ruwaito, An zo wa Annabi SAW, da wani mutum wanda ya kashe kansa da kibiya sai ya ƙi yi masa sallah.

Na huɗu. Hadisin Sabitu ɗan Dahhaku – Bukhari da Muslim. “An yi wani mutum cikin waɗanda suka gabaceku yana da ciwo sai ya kasa haƙuri ya ɗauki wani abu ya farke ciwon da shi, jini ya yi ta zuba har ya mutu, sai Allah yace : Bawana ya gaggauce ni da kashe kansa, na haramta masa aljanna “

Wanda ya kashe kansa da wani abu a duniya za a yi masa azaba da wannan abin ranar alƙiyama.

Abubuwan da suke kawo mutum ya kashe kansa:
1 Zafin talauci.
2 Rashin aikin yi.
3 Mummunar asara.
4 Tsananin ciwo.
5 Shiga wani muwuyacin hali.
6 Shan kayan maye.
7 Tsananin takaici.
8 Cin amana da yin abin kunya.
9 Tashin hankali.
10 Raunin imani.
Da makamantansu da yawa.

Abubuwan da zasu hana kashe kai.

 1. Yarda da ƙaddara.
 2. Yawan anbaton allah.
 3. Kyautatawa allah zato.
  4 tilawar alkurnani mai girma.
 4. Haƙuri da juriya.
 5. Kallon na ƙasa da kai
 6. Kula da sallah da yin ta da ilmi.
 7. Koyi da kafurai.
 8. Addu’a.
 9. Zama cikin mutane na kwarai.
 10. Ganin girman allah.
 11. Fifita lahira akan duniya.
 12. Karanta tarihi magabata.
 13. Ziyarar asibiti da kurkuku da gidan mahaukata da maƙabarta.
  Allah ka tsare mu da dukkan musulmi daga fushin allah da azabar sa.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog