/

Halacci ko Haramci: Hukuncin sana’ar P.O.S a Musulunci -Daga Sheikh Hamza Kabawa

dakikun karantawa

Taskar Malamai: Halacci ko Haramci: Hukuncin sana’ar P.O.S a Musulunci -Daga Dabo FM tare dada Shei Hamza Uba Kabawa

Da sunan Allah mai rahama da jin kai : A ƴan kwanakinnan maganganu sun yawaita akan halacci ko haramcin sana’ar P.O.S wato injin cirar kuɗi na tafi da gidan ka, wasu na fassara shi da tafi da bankin ka. Wasu daga cikin malamai suna ganin halaccinsa , wasu kuma sun tafi akan haramcinsa , gwargwadon fahimtar kowa.

Wannan sabanin kuma ya shiga tsakanin daliban ilmi da ragowar al’umma , har yake nema ya tashi daga dabi’ar sabani na ilmi , ya koma sabani wanda yai kama da siyasa. Don haka jan hankalin da zamu yi anan shi ne , ya kamata kowa ya tsaya akan fahimtarsa tare da girmama fahimtar dan uwansa.

Da farko dai ya kamata a sani ba kowane transaction na pos yake haramun ko halal kai tsaye ba , saboda transaction ya shiga babi uku :

1- Babin Wakilci ( ﺍﻟﻮﻛﺎﻟﺔ ) Wato ka sanya mai pos ya tura maka kudi daga account zuwa wani ka biya shi. Wannan babu sabani akan halaccinsa.

2- Babin bashi ( ﺍﻟﻘﺮﺽ ) Wato ka karbi bashi daga gurin mai pos , daga baya idan an turo maka kudi ya cira da kari. Wannan babu sabani akan haramcinsa.

3- Babin canji / kodago ( ﺍﻟﺼﺮﻑ / ﺍﻟﺘﺠﺎﺭﺓ ) Wato shi canjar kudi ka yi ko kuma kudinka kasa wani ya ciro su daga account dinka zuwa nasa , sannan ya baka su tsabarsu, kai kuma ka bashi lada ( Service Charges ).

A nan malamai suka saba. Wadanda suke kallonsa a matsayin canji sai suke ganin dole ne ya cika sharda na canji. Wato idan kudi jinsi daya kamar naira da naira ne su zama dai dai da dai dai , hannu da hannu. Idan kuma sun saba kamar naira da dollar to su zamo hannu da hannu kawai amma babu laifi wani ya fi wani.

Wadanda suke kallon na’urar POS matsayin kodago ne ba canji ba , suna ganin aiki ne kasa mutum ya yi maka , kai kuma ka biya shi don haka babu laifi.

A tawa fahimtar na fi gamsuwa da masu cewa pos ya fi kama da kodago ba canji ba , saboda dalilai kamar haka :
1- A bisa al’ada da abin da aka saba yau da kullum , canjin naira da naira mutane basa yi masa kallon ciniki ko kasuwanci.Duk inda ka je ka mika naira dubu don neman canji babu mai kallonka a matsayin wanda ya zo ciniki kuma kai kamka baka jin cewa ciniki ka je yi , ko ka fadi ko ka ci riba. Kowa yana kallon abin ne a babi na taimako da kyautata mu’amula. Shi yasa wanda zai bayar da canjin ba ya jin cewa kai costomer ne.
A inda kawai ake kallon mai neman canji a matsayin mai kasuwanci , sai idan ya je da naira zai canji dollar.

2- Kudi a cikin account suna da bambamci da tsabar kudin dake hannu. Don haka alakar dake tsakanin mutum da kudinsa na account , sun sha bam bam da alakarsa dake tsakaninsa da tsabar kudin dake hannunsa. Kudi a account na bukatar wasu aikace aikace da cika wasu ka’idoji kafin ka yi amfani da su , sabanin kudin dake hannunka da kai tsaye kake amfani da su. Don haka kudi a account suna kama da kadara ne ko kayan da sai an yi aiki suke zama kudi.

3- Dinare ko Azurfa sun bambamta da naira a asali da kima. Saboda Dinare ko Azurfa suna bambamta wajen kyau , nagarga nauyi da kima a jinsinsu. Sabanin Naira da matsayinta daya ne duk inda ka je. Babu bambamci tsakanin ta jiha da jiha ko gari da gari. Duk inda ka je a Nigeria matsayin Naira da Kimarta daya ne.Dinare kuwa jinsinsa da darajarsa yana bambanta. Don haka kiyasin Dinare da Naira ba a kowane babi ba ne.

Sun kama ta wani bangare , sun bambanta ta wani bangaren. Don haka raba tsakaninsu ta kowace fuska kuskure ne. Kamar yadda daidaita tsakaninsu ta kowace fuska kuskure ne. A daidaita su ta fuskar da suka yi kama , a bambamta su ta fuskar da suka saba shi ne dai dai.
A tare da cewa na fi gamsuwa da halaccin pos , amma ba ni da sabani da dukkan mai ganin haramcinsa.

Akwai nau’ikan ciniki da malamai magabata suka saba akan halaccinsu da haramcinsu. Riba ne ko ba Riba ba. Amma babu wanda ya aibanta dan uwansa. Allah ya datar da mu izuwa hanyar dai dai a duniya da lahira.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog