Shin ko kun san amfanin Danyen Kwai ga jikin dan adam?

dakikun karantawa
Danyen kwai amfani

Amfanin Danyen Kwai

Kwai ya na daga cikin nau’in abinci mafi kara lafiya a duniya. Yana dauke da sinadarai masu matukar muhimmanci da suke kara wa dan adam lafiya sosai.

Danyen kwai ya na da amfani irin daya da dafaffen kwai. Sai dai shan danyen kwai or nau’in abinci mai dauke da irin sinadaren da suke cikin kwai yana iya zama sanadiyyar kamuwa da ‘Salmonella Infection’ wani nau’in bacteria da ake samu a cikin abinci wanda yake zama sanadiyyar yin rashin lafiya.

Kazalika yana iya sanadiyyar rage wa jiki karfin karbar wasu sinadaren ko kuma ya toshe karbarsu baki daya.

Masana sun bayyana cewa Danyen kwai yana da sinadarai masu tarin yawa da jiki dan adam ke bukata.

Yana cike da sinadarin Protein mai yawa, Vitamins, Fats, wasu sinadarai masu kauda hatsari a jiki kamar kare Ido da kuma sauran wasu sinadarai da yawa.

Kwai guda daya yana dauke da sinadarai kamar haka:

  • Ma’aunin auna yawan kuzarin da abinci zai samar/ Calories (A turance): 72.
  • Protein: 6 grams.
  • Fat: 5 grams.
  • Vitamin A: Ana samun kashi 9% na daga adadin da jiki ke bukata kullum.
  • Vitamin B2 (Riboflavin): Ana samun kashi 13% na daga adadin da jiki yake bukata a kullum.
  • Vitamin B5 (Pantothenic Acid): Ana samun kashi 8% na daga adadin da jiki yake bukata a kullum.
  • Vitamin B12 (Cobalamin): Ana samun kashi 7% na daga adadin da jiki yake bukata a kullum.
  • Selenium: Ana samun kashi 22% na daga adadin da jiki yake bukata a kullum.
  • Phosphorus: Ana samun kashi 10% na daga adadin da jiki yake bukata a kullum.
  • Folate: Ana samun kashi 6% na daga adadin da jiki yake bukata a kullum.

Bayan ga wadannan sinadaren, cibiyar bayar da bayanan gwajegwajen kwayoyin halitta ta Amurka NCBI ta ce  Danyen Kwai yana dauke da Choline , wani sinadri da yake kara lafiyar kwakwalwa da zuciya. (Bincika a nanDa nan , da kuma nan).

Kazalika cibiyar ta ce Danyen Kwai yana dauke da sinadaren Lutein da Zeaxanthin wadanda suke kare ido kuma suke taimakawa wajen inganta lafiyar ido yayin da mutum yake kara shekaru (Tsufa). – duba a nan

Yana da matukar muhimmanci a san cewa yawanci wadandan sinadaren suna tattare ne a cikin Kwanduwa. Mafi yawan sinadarin da ke farin ruwan kwan, Protein ne. Don haka amfanin danyen kwai ya fi tattarewa a cikin kwanduwa.

A TAKAICE:

Danyen Kwai, nau’in abinci ne mai kunshe da sinadaran da jikin dan adam yake bukata da suka hada Protein, Fat, Vitamins da kuma sinadare masu kare jiki daga ciwo. Yana kare Ido da kuma kara lafiyar kwakwalwa. Kusan dukkanin sinadaren suna kunshe a cikin Kwanduwa.

Kwaduwar Kwai – Daga danyen kwai

Jikin dan Adam ba ya karbar sinadarin Protein na danyen kwai gaba daya.

Kamar yadda dai bincike ya nuna, kwai yana daga cikin nau’in abinci mai dauke da sinadarin Protein.

Kwai yana dauke da dukkanin Amino Acids guda 9, hakan ya sa ake kiransa da cikakken abinci mai samar da sinadarin Protein.

Sai dai shan danyen kwai yana iya rage wa jikin dan adam karfin karbar sinadarin Protein din.

Cibiyar NCBI ta kasar Amurka ta yi bincike kan yadda jiki dan adam yake karbar sinadaren da ke cikin dafaffen kwai da danyen kwai, cibiyar ta gwada hakan a jikin mutum 5.

Binciken ya tabbatar da cewa jikin dan Adam yana karbar kashi 90 na sinadaren Protien da ke cikin dafaffen kwai, in da jikin ya iya karbar kashi 50 na danyen kwai.

Kazalika binciken ya ce jikin na dan Adam yana narkar da kashi 80 na Protein da ke cikin danyen kwai.

Sai dai ana iya kashe wasu sinadaren cikin kwai idan aka dafa shi ko kuma rage musu karfi. Wadannan sinadaren sun hada da Vitamin A, Vitamin B5, Phosphorus da kuma Potassium.

A TAKAICE:Bincike ya nuna cewa jikin dan adam ya fi karbar sinadaren dafaffen kwai fiye da na danyen kwai, kazalika jikin ma ya fi iya sarrafa sinadaren cikin dafaffen kwan.

Don haka amfanin danyen kwai bai kai na dafeffen kwai ba duba da cewa jiki ya fi karba da kuma narkar da sinadaren cikin dafaffen kwai.

Duba wannan:

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog