Bankin Zenith ya tabbatar da cewa wasu masu kutse ta yanar gizo sun samu damar shiga wani ɓangare na bayanansa, lamarin da ya sa aka fallasa wasu ƙananan bayanan kwastomomi kamar adireshin imel da lambobin waya.
Sai dai bankin ya jaddada cewa ba a samu damar shiga kalmomin sirri (passwords), lambobin PIN, lambobin OTP, bayanan katin ATM ko ma’aunin kuɗin asusun kwastomomi ba. Haka kuma ya tabbatar da cewa dukkan ayyukan banki da na dandamalin dijital suna ci gaba da aiki cikin tsaro.
Rahoton Dabo FM ya bayyana cewa bankin ya gano kutsen, nan take ya aiwatar da matakan gaggawa na tsaro tare da ƙaddamar da cikakken bincike kan lamarin.
Bankin ya kuma gargadi kwastomomi da su yi taka-tsantsan da saƙonnin bogi, kira ko saƙonnin tes da ke neman bayanan sirri, yana mai jaddada cewa kada su bai wa kowa kalmar sirri, PIN, OTP ko wasu muhimman bayanan banki.
Zenith Bank ya ce zai ci gaba da ƙarfafa tsarin tsaron bayanansa domin kare bayanan kwastomomi yayin da ake ci gaba da binciken abin da ya faru.
