Shin laifi ne yaɗa ilimin jinin al’ada a kafafen sada zumunta?

dakikun karantawa
Jinin al'ada
Hoton Wkipedia

RAJASTHAN: Matsayar DABO FM na wannan makon: Shin laifi ne yada ilimin jinin al’ada a kafafen sada zumunta?

Tattauna batun jinin al’ada ga mata a kafafen sada zumunta ya dade ya na kawo cece-kuce a tsakanin al’ummar arewacin Najeriya, sai dai tambayar da take yawo shi ne; shin laifi ne tattauna irin wadannan maudu’ai?

Mafi yawan masu amfani da kafafen sada zumunta musamman a Facebook a arewacin Najeriya su kan yi wa masu yada iliman jinin al’adar mata mummunar fassara tare da kiransu sunaye marasa dadi da nufin cewar su na kaucewa koyarwar addinin Musulunci da al’adar Mallam Bahaushe.

Sai dai hakan sam ba ya tabbatuwa a matsayin laifi idan muka yi duba da yadda malaman addini suke amsa tambayoyin da suka shafi al’ada da jima’i a idon duniya.

Duk da cewar yawanci masu tattauna batun al’adar a kafafen sadarwa sun kasance matasa kuma suna bayanin al’adar ta fuskar zamani, hakan ba ya nufin sun kauce wa hanya idan har niyyarsu ta kasance da nufin yada ilimi ba don nuna dagawa ko waye wa ba.

Rashin sanin menene al’adar ma ga mata da yawa ya jefa rayukan matan Najeriya a cikin matsala, fara wa da sanin yadda jinin yake zuwa da kuma yadda ake tarbarshi cikin lafiya ba tare da an haifa wa jiki sabuwar cuta ba.

Jinin al’ada ya cika karai-rayi da camfe-camfe. Sakamakon al’adar gargajiya da rashin cikakkiyar fahimta ta addini, ya sa wasu ke kallon masu jinin al’ada a matsayin masu kazanta ko datti har ma wasu ke kallon a cikin lokacin ko kiran sunan Allah ba za su iya yi ba. Wannan dalilin ne ya sa ake ganin ayi shiru akan jinin al’ada shi ne yafi kuma kamar abin kunya ne idan aka ce mace tana yi.

Ba a iya kafofin sadarwa ba, hatta a makarantu da ya kamata a koyarwa mata ilimin jininsu na al’ada, ba a iya tattaunawa akai. Har ma a wajen wasu iyaye mata abin haka yake domin akan samu iyayen da basu san ‘yarsu ta fara ba balle su san yaushe yake zuwar mata ko tafiya.

Kazalika musamman mutanen da suke rayuwa a karkara su na shiga cikin matsanancin hali na tausayawa sakamakon rashin sanin ilimin al’ada, wasun da suka sani kuma talauci ya hana su siyan auduga domin tarbar jinin cikin kwanciyar hankali. Sakamakon hana ne yasa ba sa iya yin komai domin tsoron zubowar jinin da ba ya sanar da zuwanshi.

A wajen mazajensu kuwa, su na kyamata da tsangwamarsu, wasu sukan haramta musu shiga dakunansu ko taba kayayyakin amfanin gida musamman idan suka tina cewa ba za su iya yin jima’i da su a wanann lokacin ba.

Kazalika , sakamon rashin ilimin jinin al’ada, mata da yawa sun daina zuwa makaranta. Wasu rashin zuwan yana da alaka da rashin mallakar audugar da za ta tare zuwan jinin, wani lokacin kuma yakan zama rashin tsaftaccen bandaki da kuma rashin samar da kayyakin kariyar da idan matan sun cire audugar da suka sanyo daga gida, babu wadda za su sake sawa domin tare zuwan wani jinin.

Bisa wadannan dalilai, DABO FM na ganin cewar babu laifi idan an yada ilimin jinin al’adar mata a kafafen sadarwa wanda har maza su gani domin su ma har yanzu akwai wadanda basu fahimci menene jinin al’adar ba. Akwai buktar mazaje su samu ilimin domin ta haka ne zasu iya taimakawa matansu tare da tausaya musu idan jininsu ya zo ko za su dan huta.

A bangaren gwamnati, ya kamata ya zama hakki a kanta wajen rabawa dukkanin mata dake karkashin ikonta marasa karfi audugar mata kyauta, hakazalika ta kuma cire dukkanin haraji domin wadanda ba za su samu kyautar audugar ba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog