KULLEN KORONA: Hakuri da taimakon juna ne ya dace da mu, daga Dabo FM

dakikun karantawa

Wannan makon, daga Dabo FM.

Idan aka dauke lokutan da kasa take shiga wani hali na rikicin addini, siyasa ko wani “bore” da ya shafi wasu ma’aikata ko makamantansu, da har ake kakaba dokar ta baci, da ake cewa lakabi da “curfew”, ba a taba shiga wani yanayi da aka kulle mutane a cikin halin zullumi da fargaba a Arewacin Najeriya irin na wannan lokaci da annobar Kwabid-19 ta jefa mutane a ciki ba.

Daga kan talakawa har zuwa masu arziki, masu ilimi da akasin hakan, mutanen maraya da alkaryu, masu aikin yi da wadanda ba sa yi, ba wanda zai ce yana jin dadin wannan yanayi na kulle da aka tsunduma a ciki. Kuma ga bisa dukkan alamu ba wata rana kurkusa da za a iya hasashen ita ce ranar budewa.

Babban abin lura da fahimta a game da wannan hali da ake ciki shine, dole sai an yi hakuri da kuma taimakawa juna ta fuskoki da dama.
Akwai mata da yawa da suke shiga cikin fargaba da zarar alfijir din ranar Juma’a ya keto. Domin da zarar rana ta kusa faduwa mijinsu, ko ” dodo” zai dawo daga wajen aiki. Tun daga wannan rana ta Juma’a haka za a kasance cikin yamutsi da zullumi har ranar Litinin da safe. Daganan cikin murmushin jin dadi, za su yi sallama da magidantan, sai kuma wata Juma’ar. A haka suke ta rayuwa tare da tara zuri’a… Yanzu me ku ke zato zai kasance idan aka ce irin wadannan magidanta hukuma ta tursasu zaman dole a gida, kuma a cikin wannan matsi na tattalin arziki?

Akwai Matan da burinsu garin Allah Ya waye, su shirya yaransu, su tafi makarantar boko. Idan sun dawo da rana, a shiryasu wajen karfe uku su koma islamiyya. Wannan yanayi da ake ciki, shi yake farantawa iyayen, wajen samun hutu da nutsuwa su aiwatar da wasu lamura na rayuwa. Me ku ke hasashen halin da irin wadannan Iyaye mata za su kasance idan aka ce yaransu su na cikin gida sama da watanni kuma tare da masifaffen mahaifinsu?

Akwai mata da yawa gami da magidanta da suke futa waje domin aiwatar da wasu ayyuka na “aikatau”, a karshe da ladan aikin za su yi amfani don yin wasu hidimomin rayuwar iyalansu na yau da kullum. Wane hali irin wadannan mutanen za su kasance idan aka ce an garkame gari, ba wanda yake da ikon futa ko aiwatar da wani aiki da zai samu wani kudi don biyan bukatun rayuwa?

Idan kuwa har hakane, ashe kenan akwai bukatar baki daya mu nutsu mu fahimci halin da muke ciki.
Dole ne duk wani mai zafin rai da hasala da kakatu ko tsiwa da bambami da korafi, gami da saurin hannu da kakkausan harshe, ya yi kokari ya kimtsawa kansa hakuri da jarumta, ta yanda zai zama jarumin gaske, kamar yanda Annabi Muhammad SAW ya bayyana(duk mutumin da zai iya danne wani fushi ko hasala a lokacin da zai iya daukar wani hukunci da zai faranta masa, amma ya yi hakuri)
Irin wadannan magidanta dole su fahimci ana cikin wani yanayi na zaman makoki da kuma alhinin juna. Lokaci ne da mutum zai daure ya shiga harkokin gidansa, ta hanyar taimakawa madam wasu hidimomin rayuwar iyalansu baki daya. Wannan kadai zai kara dankon shakuwa da kuma samun nutsuwa a tattare da su.

Wadanda suke da hali ko yaya ne, kuma suka fahimci sauran bayin Allah da suke makotaka da su, kuma suke cikin yanayin “babu”, to lokaci ne da za a daure a taimakawa irin wadannan mutanen. Akwai da yawa da suna cikin yanayin fatara da talauci, amma ko da wasa ba za su taba tambayar wasu a basu wani abu da za su ci, ko su sayi wani abu da shi ba. Sai dai kawai idan mai hankali ya lura da su, ya basu dan abin da ya sawwaka.
A nan muke kara kira ga al’umma da mahukunta, kamar yanda muka yi a satin da ya wuce, idan an samu kayan tallafi ko wanda za a rabawa al’umma, da a daure a yi rabon da ya kamata, a bawa wadanda suke da ” matsananciyar” bukata. A cire siyasa da kusani, a tallafawa wadanda suka dace, kasancewar wannan wata mai falala da muke ciki.

Daga karshe Dabo FM na mai yin kira ga sauran mutane, da a daure wajen ganin ana kai zuciya nesa. Domin ba shakka wannan yanayi da aka tsinci kai, zai haifar da kunci da kuma damuwa. Karamin abu yana faruwa sai ku ga ana neman kwasar ‘yan kallo.
A daure a zama ‘yan uwan juna, a rungumi juna, a taimakawa juna, a tallafawa wadanda suke da bukata. Sauran wadanda suke da hali ko sarari da wata dama, su daure su ga sun yi amfani da ita ta hanyar da ta dace, yanda za su farantawa al’umma baki daya.

A karshe muna kara ci gaba da kira da a daure ana kula gami da lura da matakai da shawarwarin da masana kiwon lafiya ke fadi, don kariya daga wannan annoba da ake fama da ita. Komai lokaci ne, kuma nan da wasu lokuta masu zuwa, sai dai ana waiwayar wainar da aka toya a irin wannan lokaci.

Allah Ya ci gaba da karemu, Ya bamu lafiya mai amfani. Wadanda suka rasu ta wannan sanadin ciwo, Allah Ya kyautata makwancinsu, amin.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog