Ta’aziyyar Abba Kyari: Bakin Rai, Bakin Fama daga Dabo FM

dakikun karantawa

Idan akwai wani suna da ya shiga kundin tarihi na mulkin dimokaradiyya a Najeriya, kuma za a jima ana waiwayarsa wajen kafa hujjoji da bayar da bayanai game da wasu nasarori ko akasin haka, to sunan Abba Kyari ne, tsohon shugaban ma’aikata a fadar gwamnatin Najeriya karkashin mulkin shugaba Buhari.

Kafin 2015, mutane da dama musamman matasa da ke bibiyar siyasar kasar nan, ba su san Abba Kyari ba. Wata kila tsiraru ne daga cikinsu ta hanyar neman bayanai ko wata alakar, kan yi sanadin su yi kicibis da sunansa. To amma wani abu da ya zowa mutane da mamaki shine, lokacin da shugaba Buhari ya ambaci sunansa a matsayin wanda zai zamar masa shugaban ma’aikata a fadar Aso Rock (duk da cewar ofishin ba shi da cikakkiyar madogara bisa sahalewar kundin tsarin mulki, shi yasa ma marigayi shugaba ‘Yar adu’a bai yi irin wannan mukami ba), mutane da dama sun yi mamaki. Daganan ne aka fara bincike akan ko ma wanene shi.

A wancan lokacin ne aka fahimci ashe bayan an haifeshi a garin Borno kimanin shekaru 67 da suka shude, ya samu damar fita kasar Burtaniya, in da yayi karatu da dama da suka hada da ilimin sanin halayyar mutane, da kuma aikin shari’ah. Daga baya ne, ya kutsa kan sa aikin Banki a UBA har zuwa aikin Jarida da ya yi a matsayin Edita a wata jarida ta Democrats Newspaper. Bugu da kari, ya rike mukamai na kwamitoci da dama, har da su kwamishina a jiharsu ta Borno a wajejen 1990. Daga karshe ya tsunduma aiki a kamfani mai zaman kansa na Unilever bayan ya sha gwagwarmaya a cambar ‘Fani Kayode and Sowemimo’ da ke Legas (cambar mahaifin tsohon ministan jiragen sama, Mr. Femi Fani Kayode).

Daga 2015 zuwa yau, abubuwa da dama na hayaniya da kai ruwa rana, gami da zarge-zarge sun sha fitowa da ake alakantasu da Abba Kyari. Wasu kai tsaye zargi ne, wasu kuma sun tabbata a zahiri. Daga cikin abubuwan da suka fara daukar hankalin ‘yan kasa shine, badakalar Sahara energy, na wata kwangila da ake zargin marigayin ya karbi rashawa. Sai kuma batun sa hannunsa akan biyan kudin tarar da aka yi wa kamfanin MTN, an ce ya sa an rage kudin don an bashi wani abu. Akwai ma batun da sashen Hausa na muryar Amurka ya jima yana tattaunawa akai a cikin shirin Ciki da Gaskiya da Sarfilu Hashim Gumel ke yi duk Litinin, na cewar shi Abba Kyari ya bukaci wani dan uwansa ya zo a bashi kwangilar kawo motoci fadar Aso Rock, amma a karshe suka rabu baram-baram, Dutse a hannun Riga. Batun dawo da Abdulrashid Maina kan kujerarsa ta kwamitin fansho na kasa, shi ma ya jefa ayoyin tambaya akan rawar da Kyari ya taka. Akwai yamutsin da ya yi da tsohuwar shugabar ma’aikan gwamnatin tarayya Mrs Oyo-Ota, a karshe sai da ta tsinci kanta a kotu bayan ta bar kujerar ba shiri. Ruwan da suka kai rana tsakaninsa da Babagana Munguno (mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro) da kuma sabatta-juyata da ya sha da matar Buhari, su ne suka bayyanawa duniya cewar akwai wasu da ke sakale da Buhari, sai abin da suke so, ake yi, kuma hakan ne ya fito da kalmar nan ta ‘Cabal’ ko Fulogan fadar gwamnatin Buharin.

To koma dai me ake ciki, mutane da dama da suke kusa da Abba Kyari, sun sha fadin mutum ne mai amana. Kuma wannan yanayin ne ta kai shi, yake ta fafatawa da mutane. Domin kuwa idan har za ku iya tunawa, Hajiya Turai ‘Yar adu’a ta samu wani iko mai karfi da kowa sai da yayi mamakinsa. Hakanan Sambo Dasuki shima ya samu dama mai fadi da ya yi abin da yake so. Wata kila lura da wadancan dalilai ne, ya sa Abba Kyari ya hana Aisha Buhari da kuma Babagana Munguno rawar gaban hantsi, har suka zo suna tsangwamarsa a bakin duniya.

Wani abin mamaki dangane da marigayi Abba Kyari shine, abu ne mai wahala ka ji kalamansa a kafafen sadarwa duk da irin caccaka da zarge-zargen da ake masa. Kuma kamar yanda wadanda suka yi aiki da shi suke fada, wanda aka yi hira da shi a BBC Hausa, wato Badaru Abubakar, gwamnan Jigawa, ya tabbatar da cewar duk wanda aka ce sun ja layi da marigayin, to ya sabawa bukatar kasa ce, ko amanar Buhari zai ci. To koma dai ya ainahin abin yake, Abba Kyari dai ya rasu ranar Juma’a dalilin kamuwa da cutar Coronavirus ko COVID19 ranar 24 ga watan Maris din 2020. Kuma ya bar Mace daya da ‘ya’ya guda hudu; biyu Maza, biyu Mata.

Kamar yanda Ministan Sadarwa, Sheikh Pantami ya sa ran shahadar marigayin, Dabo FM ita ma tana mai addu’ar Allah Ya gafarta masa, amin.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog