Tallafin Kwabid-19: A cire Siyasa da son kai, ayi abin da Kare zai ci, Daga Dabo FM

dakikun karantawa

Tun bayan lokacin da aka fara garkame ko kulle garuruwa da manyan birane a Najeriya, gwamnati ta mike tsayin daka wajen ganin an fara rarrabawa marasa galihu dan wani abu da zai rage musu radadin halin da ake ciki. Daga cikin abubuwan da ake rabawa akwai kudade da kuma kayan abinci.

Duk da cewar rabon kudaden ya na karkashin sabuwar ma’aikatar tallafi, da su jin kai ce, Hajiyar da ke kula da ita, wato Sadiya Farouq, ta zagaya wurare da dama a yankunan Kudu maso yamma, da kuma tsakiyar Najeriya, kamar yadda hotuna da bidiyo suke ta zagayawa, ba shakka wasu da yawa sun amfana, kuma wasu da alamun abin zai yi tasiri a garesu.

Sai dai abu guda da ya fi daukar hankalin mutane shine, shin ta wacce hanya aka bi wajen futar da “ainahin” wadanda suke da muradin wannan tallafi? kuma ya rabon ya kasance? An dai jiyo amsoshi da dama wadanda ko kadan ba su sa mutane da yawa sun nutsu ba. Wata kila akan hakane, Ministan Sadarwa Sheikh Pantami ya hada baki da Hajiya Minista cewar, ai za a raba tallafin rage radadi ga kowanne dan kasa. To amma sharuddan da za a cika don mutum ya dace da karbar kudin da ake cewa wai naira dubu ashirin ne, shi ma ya tayar da wata sabuwar kurar.

Sun ce dai, wai sai wanda yake da kudi kasa da Naira dubu biyar a asusun ajiyarsa a Banki ne, hakanan wanda ya sawa lalitar wayarsa kudi wanda bai wuce naira dari uku ba, ta asusunsa, wai shi ne kawai zai dace da samun tallafin. Mutane da dama sun yi dariya da wannan batu, kuma ba shakka mu ma wannan tsari ba mu yi na’am da shi ba.

Idan aka dauke batun rabon kudi, da za a iya cewa ana ta ci gaba da yinsa a wani tsari da su kansu ‘yan majalissun kasa ke inkarin yanda ake yinsa, akwai batun rabon kayan abinci da suka hada da Shinkafa, Masara da su Taliya, Mai da dai sauransu, wanda ake zaton idan talaka mara karfi ya samu, zai ji ‘yar sawaba a tattare da shi a wannan hali da ake ciki.

A cikin kwanaki goma da suka shude, an tura irin wadannan kayan abinci yankunan Yarabawa. Idan har ba surutu ne irin na mutane ba, an jiyo gwamnan jihar Oyo na cewa shinkafar da aka bashi(wacce aka turo daga wadanda hukumar kwastam take kwacewa), wai ba ta da kyau. Ta lalace, kuma za ta iya kawo matsala ga lafiyar mutanen da suka ci ta. Amma dai bayan kwanaki ba wani sabon abu da aka kuma ji, wata kila an yi abin na mu(kashe magana don bukatat masu iko)

To koma dai ya abin yake, kuma ya komai ya kasance da ci gaba da faruwa, a wannan lokacin, motoci masu yawa cike dam da abinci sun iso Kano. Kuma sako ne kai tsaye daga shugaban kasa Buhari zuwa ga mutanen jihar Kano da su ma kullen ya ke ci gaba da garkamesu a gidaje.

An ce kayan abinci marasa karfi za a rabawa, sai kuma wadanda suke da bukata ta musamman haka. Wanda hakan ba karamin abin ayi murna ba ne, ganin ana sa idanu akan rayuwa da kuma walwalwar wadanda ake mulka.

Sai dai da yawa daga cikin shugabanni da suke kan iko, ba sa tsayawa su fahimci ainahin wane kayane ya kamata a sa masa son zuciya ko kallo na siyasa, kuma wanne ne bai dace da hakan ba?

Bari mu baku misali, kayan da dan majalissar PDP ko APC ya kawowa mazabara, to irin wadannan kayayyakin ne za a samu shugabannin mazabu da na jam’iyya, za su yi dakan-daka, shikar-daka. Wato dai ayi abin nan da ake cewa tuwona, mai na. A zabi wadanda ake so a bawa, wata kila masu yin aringizon bukatar manufar jam’iyya ce da dan takara, kana a basu abin da aka ga dama.
Abu na biyu shine, a lamari irin na annoba ko musifa da wata matsala da ta shafi al’umma baki daya, to batun nuna bangaranci na siyasa ko son zuciya ba karamin kuskure da ganganci ba ne.

Tun da dai tallafin ya shigo ne daga gwamnatin tarayya, to ana so a shiga sako da lungu na unguwa a zakulo wadanda ake da tabbacin suna da bukata, kana a rarraba musu abin da ya sawwaka. Domin a lokacin shan rantsuwa ta shugaban kasa da gwamna, sun yi alkawari irin haka, na kare rai, walwala, dukiya da kuma zaman lafiyar al’umma, sai uwa uba adalchi da daidaito.

Kiran da Dabo FM ta ke yi shine. duk da an tsinci kai a wani tsini na tasirin adawar siyasa, to ayi ta ‘yan Maza a daure a raba komai da komai a kan adalchi, yanda kowa da kowa zai ji dadi yace madallah.
Wannan ne abu guda daya da gwamnati za ta yi ta farantawa al’umma baki daya.

Idan har aka samu wani akasi, duk da ba fata ake ba, to ba shakka ba karamar rawa zai taka ba, wajen bijiro da wasu abubuwa marasa dadi, da za su iya jefa kowa da kowa cikin matsala da wani yanayi mara tabbas.
Don haka abu ne mai kyau, malamai da sauran kafafen sadarwa, su daure su hada baki wajen kiran mahukunta ayi abin da ya kamata a lokacin da ya dace!

Karin Labarai

Sabbi daga Blog