Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim Khalil ya ce babu laifi a kan wanda ya bayar da cin hanci idan an tilasta masa don ya samu aikin da ya san ya cancanta.
Ya ce wanda ya bayar a wannan yanayin, babu laifi a kan shi sai dai wanda ya karɓa kuma ya ci haram.
Malamin ya bayyana haka ne yayin da ya ke amsa tambayar da wani ya yi masa a wani shiri da ya gabatar wanda DABO FM ta saurara ranar Laraba a gidan Rediyon Freedom da ke jihar Kano.
Sai dai malamin ya jaddada cewa haramun ne mutum ya bayar da cin hanci idan ya san bai cancanci aikin ba.
Haka kuma ya ce haramun ne idan mutum ya san akwai waɗanda suka fi shi cancanta, amma ya bayar da cin hanci domin a hana su aikin, shi kuma a ba shi.