Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Arewa nada bukatar Jagororin irin Kwankwaso – Sheikh Ibrahim Khalil

2 min read

Arewa ta na da bukatar jagorori irinsu Sanatan Kano ta tsakiya, Engr Rabi’u Kwankwaso duba da irin yadda Arewa ta tsinci kanta a yanayi na rashin jagora mai kishin al’umma da kuma fada a ji a wannan yankin na arewa.

Jaridar Leadership Hausa ta rawaito maganar Malamin a wata hira da wakilinta yayi da Sheikh Ibrahim Khalil.

“Babbar matsalar da yankin (Arewa) ke fama da shi a Najeriya a halin yanzu shine rashin jagora guda daya wanda zai jagoranci al’umma zuwa ga tudun mun tsira.”

Ya kara da cewa, duk wanda aka kawo akace a saka shi a gaba a matsayin shine jagoran yankin wanda za’a rika girmama umarninsa, sai ka ga an rufar ma sa da sara da suke na batanci, ya na mai cewa hatta wanda ya kawo sunan jagoran shi ma ba zai tsira daga sharrin magauta ba, sabanin yankin Yarabawa da ke kudu maso Yamma, wadanda a koda yaushe su ke yin biyayya ga jagoransu a kan alkibla guda daya tun daga kan Awolowo har zuwa.

Arewa na da bukatar mutum irinsu Kwankwaso jajurtattu, masu gaskiya da rikon amana, wadanda ba sa yaudara kuma ske da cikakkun tsarin da zai dore.

 

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.