/

Rahama Sadau: Hakkin Manzon Allah SAW ba ya saraya da tuba – Sheikh Hamza Kabawa

dakikun karantawa

Taskar Malamai daga Dabo FM tare da babban limamin masallacin Bello Road dake Kano, Sheikh Hamza Uba Kabawa

Daga abin da ya kamata al’umma su sani shi ne : Duk abin da ya shafi taba Mutuncin manzon Allah S.A.W. ba ya sarayar da shi. Dalili kuwa shi ne akwai hakkoki guda uku cikin taba mutuncinsa.

1- Hakkin Allah

2 – Hakkin shi kansa Manzon Allah.

3 – Hakkin muminai.

Hakkin Allah yana saraya da tuba. Amma hakkin manzon Allah sai dai shi ya yafe maka. Kamar a lokacin rayuwarsa. Ya yafe wa wasu da suka taba mutuncinsa. Ya kuma tsayar da haddi a kan wasu.

Amma kasantuwar yanzu ya koma ga Allah , babu wata hanya da zai yafe da kansa.

A kan haka bayan rasuwar Manzon Allah tuba ba ya sarayar da hakkin Manzon Allah. Wadancan hakkoki guda uku suna nan daram. Wannan shi ne ra ayin da Ibn Taimiyya ya rinjayar a littafinsa “Sarimul Mas’lul Ala Shatimir Rasul ” 2/438

Manufar wannan rubutu shi ne jan hankalin al’umma da suke ganin idan an taba mutuncin Manzon Allah da an tuba shi ke nan. Ko masu cewa su sun yafe hakkin da ba nasu ba.

Mutuncin Manzon Allah babu mai yafe shi sai shi da kansa.

Tun da kuma ya koma ga Allah , babu abin da ya yi saura sai hukunta wanda ya aikata ko ta jawo aka aikata gwargwadon abin da shugaban musulmi ya ga zai fi zama mas’laha da jan kunne ga yan baya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog