Halaccin aurar da matasa da zawarawa daga kudin Zakka -Tare da Sheikh Hamza Kabawa

dakikun karantawa

Shirin Taskar Malamai na Dabo FM tare da babban limamin masallacin Juma’a na Bello Road, Sheikh Hamza Uba Kabawa.

Sanin kowane cewa zawarci da gwagwarci na daga cikin manyan matsalolin zamantakewa. Duk al”ummar da zawarawa da gwagware suka yi yawa a cikinta to babu makawa sai ta tsunduma cikin matsala.

Idan mutum ya yi duba na tsanaki zai ga cewa mafi yawan matsalolin dake faruwa na shaye shaye da lalata kamar neman mata ko maza ko madigo da ragowar miyagun laifuka suna da alaka ta kai tsaye da yawan mutuwar aure da yawaitar zawara da gwagware a cikin al’umma.

Babban kuma abin dake taimakawa wajen yaduwar zawarwa da gwagware bayan talauci da jahilci akwai buri , karya , son abin duniya da kwadayi.

Za a iya cewa ma, gudunmmawar da wadannan abubuwa ke bayarwa wajen yaduwar barna da gwagwarci har ta fi ta talauci. Samari da Yan mata da yawa sun sanya karya da buri a zuciyarsu. Sun sami mazajen aure amma sun raina.

A yau ba a jiya ba akwai yan mata yan shekara talatin da biyar zuwa arbain. Ba kuma wai don sun rasa mazajen aure ba ne tun da farko. A a dai donsun sa buri ne kawai a zuciyarsu.

Akwai samari da yawa da suka sa buri a zuciyarsu cewa sai irin kalar mace kaza ko yar gidan kaza zasu aura. Wasu basu da koda fili amma suna lissafin unguwanni masu tsada da sai a su zasu zauna.

Sabanin rayuwar magabatanmu da suka dauki rayuwa da sauki. Sai komai ya zo musu da sauki. Mu kuwa da muka dauka da zafi sai komai yake zuwar mana da zafi.

Bamu ce dukkan Samari da Yan mata haka suke ba. A cikinsu kam akwai wadanda suka dauki rayuwa da sauki , illa iyaka idan matsala ta game al’umma ta kan shafi wanda ya jawo ta da wanda bai jawo ta.

Akan haka muke kira ga mawadata da masu iko da su dinga duba matasa da yan mata da zawaran unguwanni suna tallafa musu wajen aure koda da kudin zakkarsu ne.

Akwai aure da yawa a halin yanzu da ake ta dagawa saboda babu yadda za a yi.
Malamai sun bayar da Fatawar cewa ya halatta a tallafawa masu neman aure da kudin zakka. Akwai matasa da yawa da zasu iya rike aure , amma basu da karfin daukar dawainiyar aure.

An tambayi babban malami Sheikh Usaimin Allah ya ji kansa kan halaccin tallafawa matasa don su yi aure da kudin zakka sai ya ce : ” Hakika ya halatta a aurar da mutum da kudin zakka. A biya masa sadaki da dukkan wahalhalun aure.

Sannan sai ya ce : ” Hikimar yin haka ita ce bukatar aure a gurin mutum tana da karfi. Dai dai take da bukatarsa ta abinci ko abin sha. A wani lokacin ma har tafi bukatar abinci da abin sha. Akan haka malamai suke cewa : wajibi ne akan mutum ya aurar da wadanda suke karkashin kulawarsa idan basu da karfin yin aure. Wajibi ne akan uba ya aurar da dansa – ko yarsa – idan suna da bukata kuma ba shi da karfin yin aure.

Amma nakan ji labarin iyaye da basa Kula da matasansu suna kin aurar da dansu a halin yana bukata. Sai su ce ya yi aurensa da kudinsa. Wanna bai halatta ba , Kuma haramun.

Wajibi ne mutum ya aurar da dansa idan yana bukatar aure matsawar yana da iko.
Idan kuwa yaki to ya sani lalle zai yi rigima da dansa ranar Alkiyama akan yana da ikon ya aurar da shi amma ya ki.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog