Hanyoyi 3 da za ku iya shiga Rawdah cikin sauki

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

Masallacin Madina na daga cikin manyan wuraren da aka fi ziyarta a duniya domin yin sallah da kuma ziyartar Manzon Allah (SAW).

Kusan duk masu zuwa Umra ko aikin Hajji su na zuwa Madina domin wannan ziyara. Wasu su kan fara zuwa Madina kafin su wuce Makkah, wasu kuma su fara zuwa Makkah, sannan su je Madina kafin su koma ƙasashensu.

A cikin Masallacin Manzon Allah (SAW) ne Raudha ta ke, wato ainahin wurin da ke tsakanin ɗakin Manzon Allah (SAW) da mimbarinsa. Ya zo a cikin hadisi cewa tsakanin mimbarinsa da gidansa akwai wani ɓangare daga cikin gidan Aljanna.

Bayan ɓullar cutar Korona a shekarar 2020, ƙasar Saudiyya ta takaita masu shiga Raudha, har ma daga bisani ta sanya cewa sai mutum ya nemi izini kafin a bar shi ya shiga.

Wannan mataki ya shafi kowa, mazauna Madina da kuma alhazai.

Ga hanyoyi 3 da za ku bi domin samun shiga Raudha:

Hanya ta ɗaya:

Mutum zai yi amfani da manhajar Nusuk, ya shiga wajen neman izini, ya nema, sannan ya zaɓi rana da lokaci. Idan ya rage saura awa 2, zai ga izinin ta hanyar ‘QR Code’, wanda zai nuna wa masu tsaron ƙofa kafin ya shiga.

A ƙa’idar wannan hanyar, sau ɗaya a ke amfani da ita, kuma ba za a sake yin amfani da ita ba sai bayan shekara ɗaya.

Hanya ta biyu:

A tsarin neman izinin shiga Rawdah, kamar yadda mu ka faɗa a hanya ta farko, cewa ana iya samun izinin shiga ne sau ɗaya a shekara. Mutum ɗaya, waya ɗaya a cikin shekara ɗaya.

Sai dai Saudiyya ta yi la’akari da mazauna birnin, inda ta ga bai kamata mutum ya kasance a garin ba, amma ya shiga sau ɗaya kacal a shekara.

Sai ta fito da tsarin Instant Booking, ma’ana neman izini kai tsaye.

Yadda wannan tsarin yake shi ne, mutum zai yi amfani da manhajar Nusuk idan ya kasance yana kusa sosai da Haramin Madina. Sai ya je wajen booking ya jira. Duk minti ashirin ana buɗe bayar da izini. Idan adadin mutanen da ake nema bai cika ba, alamar tauraro mai launin kore za ta fito. Sai ya yi sauri ya danna. Idan masu neman izinin ba su cika gurbin ba, zai samu izinin nan ta ke.

A rana, mutum sau ɗaya kacal zai iya yin hakan.

Hanya ta uku:

Wannan ta shafi masu zuwa Madina tare da kamfanin zirga-zirga. Kamfani yana da damar nema wa alhazansa izini ta hanyar samo musu izinin tawaga, kuma mutum zai iya shiga ta wannan hanyar.

Saboda haka, idan kun bi kamfani, lallai ne ku yi musu magana domin su nemo muku wannan izinin tawaga.

Muhammad Dangalan ne ya rubuta. Ya Alhaji, idan Allah Ya sa ka samu damar shiga, ina roƙon addu’a daga gareka. Kuma kar a manta da yi wa ƙasar Najeriya addu’ar samun zaman lafiya da shugabanni na gari.

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00