Asibitin Aminu Kano ya fitar da sabon jadawalin zuwa dubiyar marasa lafiya a asibitin

by Dabo Online
0 comments

Asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano da ke jihar Kano ya fitar da sabon daftarin yadda masu zuwa dubiya za su riƙa shiga asibitin.

DABO FM ta tattara cewar a cikin sanarwar, asibitin ya sanar da lokacin zuwa dubiyar da kuma tsarin da za a riƙa bi wajen samun izinin shiga dubiyar marasa lafiya a cikin asibitin.

Sanarwar ta ce daga za a riƙa barin masu dubiya su shiga asibitin ne da misalin ƙarfe 4 na yamma har zuwa 6 na yamma a duk ranakun Litinin zuwa Juma’a. Ma’ana waɗannan lokuta ne kaɗai aka amince domin zuwa dubiyar a cikin ranakun.

A ranar Asabar da Lahadi kuwa, marasa lafiyar za su iya shiga daga ƙarfe 12 na rana har zuwa ƙarfe 6 na yamma.

Sai dai a cikin sabon tsarin, asibitin ya sanar da cewa; Mutum 2 kacal ne za su iya shiga duba mara lafiya a lokaci guda. Kazalika, asibitin ba ya son a riƙa shiga da yara yan ƙasa da shekara 12 ko dan saboda lafiyarsu.

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00