Abin da ya kamata ku sani game da Cutar Mashako ‘Diphtheria’

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments
cutar mashako

Menene Cutar Mashako?

Cutar Mashako wadda aka kimiyyance ake kira da Diphtheria, cuta ce mai tsanani da ƙwayoyin cuta na bakteriya ke haifarwa wadda ke kama maƙogwaro, hanci, wani lokacin ma kuma tana kama fatar jiki.

Ɓarkewar cutar Mashako a Najeriya

Hukumar Yaki da Cutuka Masu Yaduwa ta Najeriya NCDC ta bayyana cewa an fara samun ɓarkewar cutar mashako a shekarar 2011 a jihar Borno inda mutum 98 su ka kamu da cutar, 21 kuma daga cikinsu suka rasa rayukansu.

A wannan lokacin, NCDC ta ta’allaƙa ɓarkewar cutar da mutuwar da aka samu da rashin samun ishsshen rigakafin da ake yi wa yara da rashin gane cutar a matakin farko, kuma rashin wayar da kai game da cutar da kuma rashin allurar DAT da maganin Antibiotics.

Alamomin Cutar Mashako

Daga cikin manyan alamomin cutar daga farko-farko, sun haɗa da:

  1. Zazzabi
  2. Yoyon Hanci
  3. Shaƙewar Maƙoshi
  4. Jajayen Idanu
  5. Kumburin Wuya
  6. Tari
  7. Fitowar wani abu kamar kakide da ke toshe maƙoshi.

Sai dai a yara kamar jarirai, ana iya gane alamar cutar ne idan suka ƙi ƙarɓar nono daga mahaifiyarsu.

Ta yaya Mashoka ke watsuwa?

Kamar yadda aka muka faɗa a baya cewar, cutar mashoko, cuta ce da wata ƙwayar cutar bakteriya ke haddasawa don haka ta na da saukin yaɗuwa. Cuta ce da ake ɗauka kuma ake iya yaɗata a cikin al’umma. Ga jerin ta yadda cutar ke watsuwa a cikin al’umma:

  1. Cuɗanya da mai cutar.
  2. Shaƙar numfashi, tari ko atishawar mai ɗauke da cutar.
  3. Amfani da tufafi ko kayan da mai cutar ya yi amfani da su.

Ta yaya za ku kare kanku daga cutar Mashako?

  1. A tabbatar da an yi wa yara rigakafin cutar.
  2. A yawaita wanke hannu da sabulu da ruwa mai gudana.
  3. A hanzarta kai wanda aka ga alamomin cutar sun bayyana garesu zuwa asibiti mafi kusa.
  4. Kula da tsaftar kai da kuma muhalli.

Menene maganin cutar Mashako?

Dole ne aje asibitin wajen jami’an lafiyar da aka ware domin kulawa da masu ɗauke da ciwon. Ana maganin cutar mashako ne ta hanyar yin allurar DAT wadda ake cewa Diphtheria Antitoxin, sannan kuma kasancewar musababbinta ƙwayar cuta ce, ana bada maganin Antibiotics domin ya kassara da kuma kashe ƙwayar cutar daga cikin mai ɗauke da cutar.

Jihar Kano ce ta kan gaba wajen samun yawaitar cutar mashako a Najeriya.

 

 

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00