Babbar Ministar ma’aikatar ayyukan jinkai da bala’i a Najeriya, Hajiya Sadiya Umar Faruk ta koka kan yadda ta ce ake yada labaran karya a kan maganganun da bata fada ba.
Ministar ta ce “idan mafadin magana wawa ne, majiyin magana ba wawa bane”.
DABO FM ta tattara cewar ministar ta bayyana haka ne a ranar Litinin 3 ga Agusta a taron jawabai na kwamitin shugaban kasa kan cutar Korona don fayyace bayanai sakamakon jita-jita da tace ana yadawa kan shirin ciyarwa da gwamnati take yi.
Minsitar tayi bayanin kan yadda tsarin ciyarwa yake gudana, inda ta bayyana cewa bisa kidudduga, kowane dalibi yana cin abincin 1400 a wata tin daga lokacin da aka fara dokar kulle a Najeriya.
Kalli bidiyon a nan: