/

Cutar Korona ka iya zama ajalin mutane miliyan 2 – WHO

Karatun minti 1

Hukumar Lafiya ta duniya ‘WHO’ ta ce akalla mutane miliyan biyu ka iya mutuwa idan har kasashe da sauran hukumomin lafiya suka kasa yin duk mai yuwawa wajen dakile cutar Koranbairas.

DABO FM ta tattara cewa zuwa yanzu mutane kusan miliyan 1 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Koronabairas tin bayan barkewarta daga birnin Wuhan na kasar Sin.

Dr Tedros Adhanom – Darakta Janar WHO (Hoto: Getty Images)

A wani rahoto da gidan Rediyon Faransa ta yi, ta ce hukumar WHO ta yi gargadin karuwar samun wadanda za su mutum bayan da cutar Korona ta sake ta’azzara a wasu kasashen duniya bayan lafawarta a kwanakin baya.

 

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog