Kwabid-19: Za a fara gwaji kan mutane na rigakafin da aka samar a Birtaniya

dakikun karantawa

Masana ilmin kwayoyin cuta a jami’ar Oxford sun kirkiri rigakafin cutar Koronabairas da ta addabi duniya.

Za a  fara gwajin rigakafin kan mutane ranar Alhamis mai zuwa.

Wannan ya biyo bayan wanda kasar Sin ta samar kuma ta fara gwaji, sai dai  har kawo yanzu basu bayyana sakamakon ba.

Sakataran kiwon lafiya na kasar Birtaniya, Matt Hancock, ya bayyana cewa an samar da rigakafin cutar Kwabid-19 kuma ranar Alhamis za’a fara gwadawa kan masu cutar.

Masana ilmin Kimiyan jami’ar Oxford ne suka kirkiri rigakafin mai suna ”ChAdOx1 nCoV-19″

Yayin da  yake jawabi a taron da aka shirya a fadar Firaministan kasar Burtaniya, Hancock ya ce gwamnatin na iyakar kokarinta wajen samar da rigakafin cutar COVID-19.

Ya ce gwamnatin ta bai wa masana ilmin Kimiyar Jami’ar  Oxford, yuro milyan 20 (N.9.5bn) domin taimakawa wajen gwajin rigakafin.

Hancock ya kara da cewa;  za a kara bai wa wasu masana kimiyar na jami’ar Imperial College dake Landan £22.5 million domin nasu binciken.

Ya ce gwamnatin “za ta basu dukkan goyon bayan da suke bukata da kudi har su cimma burin samun nasara cikin kankanin lokaci.”

“Kuma daga karshe, hanya mafi inganci na kawar da cutar Korona ita ce samar da rigakafi. Wannan sabuwar cuta ce, bamu san yadda za a kare ba, amma ina da tabbacin za muyi iyakar kokarinmu wajen samar da rigakafin.”

“Kasar Ingila ce ke kan gaba wajen neman rigakafin a duniya. Mun fi kowace kasa a duniya zuba kudi wajen binciken nemo rigakafi.”

“Kuma duk da kokarin da sauran kasashen duniya ke yi, biyun da ke kan gaba a nan suke, Oxford da Imperial.”

“Bisa da dukkan kokarin nan da muke yi, ina mai sanar muku da cewa za a fara gwajin rigakafin da aka kirkiro a jami’ar Oxford ranar Alhamis.”

“Gaskiya samun irin wannan nasara kan dauki shekaru amma ina alfahari da aikin da suka yi.”

“Ba tare da bata lokaci ba, zamu zuba kudi domin kara samar da rigakafin da yawa idan an samu nasara tayi aiki.”

Amma ya bayyana cewa har yanzu babu tabbas.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog