Har cikin ma’ajiyar kudade Goggon Birin yabi ya hadiye miliyan 6.8 a jihar Kano

Har cikin ma’ajiyar kudade Goggon Birin yabi ya hadiye miliyan 6.8 a gidan namun dajin gwamnatin jihar Kano.

Wani ma’aikacin gidan namun dajin daya bukaci a sakaye sunanshi ya bayyanawa gidan Rediyon Freedom dake jihar Kano cewa Goggon birin ya dakawa kudaden wawa a ma’ajinsu.

Da yake bayani, shugaban tattara kudaden shiga na gidan, ya bayyana faruwar al’amarin.

DABO FM tace shugaban tattara kudaden na gidan namun dajin ya bayyanawa sashin BBC cewa kawai kudaden sun bata ne kuma ana cigaba da gudanar da bincike akan lamarin.

Shugaban dai yaki bada tabbaci ko rashinshi akan cewa wani goggon biri ne ya dakawa kudaden wawa kafin daga bisani ya hadiye su.

Masu Alaƙa  Har yanzu Abba Kabir Yusuf muka sani a matsayin dan takarar gwamnan PDP - INEC

Itama a nata bangaren, Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin.

DSP Haruna Abdullahi, ya ce tini dai sunyi kame ma’aikatan gidan namun dajin su 10 tare da mika su zuwa ga hukumar CID.

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: