0
Sanata Babayo Garba Gamawa dan adalim jihar Bauchi a Najeriya ya rasu a asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Bauchi dake garin Bauchi.
Gamawa ya rasu yanada shekaru 53, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya a yammacin Juma’a.
Mai magana da yawunshi, Isah Garba ne ya sanar da Jaridar Daily Trust.
Kafin rasuwarshi ya kasance Sanata mai wakiltar yankin Arewacin Bauchi a majalissar dattijan Najeriya daga shekarar 2011-2015 a karkashin inuwar jami’iyyar PDP.
