(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Ko wane irin mataki masu madafun iko suke dauka wajen ceto rayuwar Sheikh Ahmad Suleiman?

Karatun minti 1

Yau Talata 19/03/19, kwana 4 kenan tin bayan dauke babban Sheikh, Gangaran, mai daddadar kira’ar karatun Al-Qur’an na wannan zamani namu a kasar Hausa, Mal Ahmad Suleiman akan hanyarshi daga Birnin Kebbin Najeriya.

Iyalan gidan malamin, tare da wasu manyan malamai sun tabbatar da faruwar al’amarin.

A wani sautin muryar da yake ta yawo a gari, wanda ake zaton tattaunawar Sheikh Ahmad ce ta farko tin bayan da ‘yan bindigar suka dauke shi. Sheikh Ahmad ya tattauna da Malam Nasiru Gwandu inda ya bukaci al’umma su sakashi a addu’o’insu.

Ya kara da cewa yana cikin matsanancin hali, inda har ya bukaci a siyar da ‘yan gidajen daya mallaka a jihar domin ceto rayuwarshi. Subhanallah.

[irp posts=”4647″ name=”‘Yan bindiga sun sace Sheikh Ahmad Suleiman Kano”]

Wane irin matakai shugabanni suke dauka wajen ceton wannan Hafizin Al-Qur’ani daga kangin magauta?

A dai-dai wannan lokaci da ake ruguntsumi na zaben gwamnoni musamman a jihohin Kano, Bauchi, Adamawa da Filato. Al’umma na ganin wasu bada dauki wajen biyan dukin diyyar da ‘yan bindigar zasu bukata.

Sai dai wasu na ganin yin hakan zai nuna gazawar tsagin gwamnati wajen tabbatar da tsaro a ban kasa.

Anata kira ga malamai a masallatan Juma’a dama wuraren tarukan addinin musulci da kuma duk musulmi idan ya tashi yin addu’a, ya saka Ya Sheikh a ciki.

Fatan dai Allah ya bayyana Sheikh ya kuma tona asirin duk wadanda suke da hannu a cikin wannan ta’asar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog