Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Gwamnatin Tarayya zata kara kudin Haraji bayan da Majalissar Dattijai ta aminta da biyan N30,000

1 min read

Gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar tattara haraji ta Najeriya (FIRS) tace ‘yan Najeriya su shiryawa karin kudin harajin da suke biya.

Karin Kudin harajin  na VAT zai tashi daga kaso biyar da ake biya zuwa kaso 7.25.

Da suke jawabi a gaban kwamitin ma’aikatar kudi ta kasa, shugaban hukumar tattara harajin, Mr Babatunde Fowler tare da wasu manyan ma’aikatan hukumar, sun bayyana cewa lallai al’ummar Najeriya su san da shirin karin kudin harajin da suke biya, biyon bayan karin kudin albashi mafi karanci zuwa N30,000.

Yace zasu kara harajin ne domin cimma manufar su ta tara wa asusun Najeriya kudin daya kai Tiriliyan 8 a karshen shekarar 2019.

Kamfanin dilancin labarai na NAN ya rawaito cewa kwamitin da ma’aikatar kudi ta shirya ya zauna ne domin bada bayanai akan shirin su na kudirin da suka dauka na tsara kashe kudin Najeriya daga shekarar 2019-2021.

Karin kudin haraji na VAT ya biyo baya ne a dai-dai lokacin da majalissar Dattijan kasa karkashin jagorancin Shugaban Majalissar, Dr Bukola Saraki, ta amince da karin albashin mafi karancin ma’aikaci a fadin Najeriya zuwa N30,000 a kowanne wata.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.