Mon. Nov 18th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Zainab Aliyu ta dawo gida Najeriya

2 min read

Zainab Aliyu ta dawo gida Najeriya ne bayan ta shafe fiye da watanni hudu a tsare a wajen hukumomi Saudiyya.

Ta dawo kasar ne a safiyar Litinin 13 ga watan Mayu da misalin karfe 10:00 na safe inda ta sauka a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano (MAKIA) da ke birnin Kano.

Tun a watan Disambar bara ne dai jami’an tsaro a kasar Saudiyya suka kama Zainab Aliyu jim kadan bayan isarsu kasar domin yin aikin Umara ita da mahaifiyarta Maryam da kuma ‘yar uwarta Hajara.

Jami’an tsaron sun zarge ta da safarar kwayar Tramadol har guda 2,000 bayan da aka ga kwayoyin a wata jaka mai dauke da sunanta.

Sai dai daga baya da aka zurfafa bincike hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta NDLEA ta gano cewa wasu ma’aikata ne a filin jirgin saman MAKIA suka saka mata kwayar a jakarta.

Kwamandan hukumar mai kula da MAKIA Ambrose Omorou ya tabbatar wa da BBC cewa tuni suka kama mutum shida, wadanda ake zargi da aikata hakan.

Uku daga cikinsu ma’aikata ne da ke tantance kayayyakin matafiya, daya ma’aikacin wani kamfanin sufurin jirgin sama ne, sauran biyun kuma jamai’an tsaro ne a filin jirgin saman.

BBC HAUSA

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.