Labarai

Mutanen Gama su fara koka wa kan ayyukan da Gwamnati taki cigaba da yi a yankin

Mazauna unguwar Gama daka Kano sun koka kan ayyukan da Gwamnan Kano ya fara kuma bai kammala ba yayin zaben cike gurbi a mazabar da akai a yayin zaben 2019 da ya gabata.

Auwal Danlarabawa daya daga cikin mazauna unguwar Gama ya bayyana kokensu kamar haka:

Burtsatsen Masallacin Yara layin Makarantar adfalu tunda aka haka aka barta ba tare da an saka solar ba Ballantana Batir zuwa karasa ta yadda Za’a anfana da ita kuma mun san yadda akayi kokarin wannan aikin Dan a Tallafawa Al’umma musanman akan Matsalar ruwan Sha da ake fama dashi a Mazabar Gama. 

Dama wasu kuma muna Kara Kira da a duba solar din da aka Sakawa Burtsatsen Dan akwai bukatar ya zama kowacce tana da Batir kamar yadda ka umarci Ayi ingantaccen aiki wanda Za’a Dade ana anfani da tagomashin da ka kawo wannan Mazaba. 

Muna Fatan Za’a duba wannnan koke tare da share mana Hawaye Dan kar a cigaba da cewa Rijiya ta bayar guga Ya Hana.”

Daily Nigerian Hausa

Karin Labarai

Masu Alaka

Ganduje ya kori mota cike da ‘yan cirani zuwa Kano daga Abuja

Dabo Online

Yanzu-Yanzu: Jiga-jigen APC sun dira a Habuja da duku-duku kan shari’ar zaben Kano

Muhammad Isma’il Makama

Kungiyoyin ‘masu kishin Kano’ guda 35 sun nemi in ya sauke Sarki Sunusi – Ganduje

Dabo Online

Sakamakon zaben Gama ya ɓace ne a cibiyar tattara sakamako dake karamar hukuma – Baturen Zabe

Dabo Online

Ra’ayoyi: Buhari a dafa su, Ganduje a soya su – Matashi

Dabo Online

Ganduje ya janye biyawa Dalibai kudin jarrabawar NECO

Dabo Online
UA-131299779-2