Home Ra'ayoyiRa’ayoyi: ‘Shugabanni ne ke koya wa al’umma karya doka’

Ra’ayoyi: ‘Shugabanni ne ke koya wa al’umma karya doka’

by Dabo Online
0 comments

Ra’ayoyi: DAGA NA GABA… Tare da Ahmad Muhammad Nass.

RAYUWA= Wata aba ce mai matukar muhimmancin gaske ga kowace halitta, musamman halittu ma’abota hankali, abin nufi dan’am da aljanu. Domin kuwa a cikinta ne ake samun damar yin abubuwan da za su amfanar da zantakewar wannan duniya da gina ingantacciyar makoma bayan mutuwa.

Hakika wannan ba zai samu ba har sai an samu damar yin rayuwar cikin yanci, walwala da salama. Idan muka duba Al-qur’ani mai tsarki A cikin sororin Ma’ida aya ta 32,5, 2, An’am aya ta 151, Dhariyat aya ta 19 Nisa’i aya ta 135, duk sun yi managa kan yancin bari a rayu, ko taimakawa rayuwa ta tafi bisa adalci ba tare da tsangwama ba.

Kazalika kundin tsarin mulkin kowace kasa ya ba yan kasa yanci da ya zama wajibi a kiyaye masu.

Misali: A Najeriya kundin tsarin mulki na 1999 da ake amfani da shi a yanzu, ya yi wasu tanadi ga yan kasa ta yanda ya nuna suna da yanci. Idan aka duba sashi na hudu ya ce dan kasa yana da yanci kamar haka;
Yancin Rayuwa: A saɗara ta farko a karkashin wannan bangare an ce mutum yana da damar ya rayu babu wani mutum da aka sahalewa ya hana mutum rayuwa.
Yancin Martaba Mutumtaka: A sakin layi na farko (a), (b), da (d) an ce “ba a yardarwa wani ba ya azabartar ko nuna rashin tausayi ko bautarwa ko tilasci a aiki ga wani ba”.
Yancin Walwala: Wannan sashi ya bawa dan kasa damar yin walwala daidai da ra’ayinka da doka ta sahale, a karkashin wannan bangare a sakin layi na (2) ya ce: “duk mutumin da aka kama, ko aka tsare, yana da yancin yin shiru ko kin amsa kowace tambaya har sai bayan tuntubar lauyansa ko wani mutum ba bisa tilasci ba”.

Yancin kare sirrin dan kasa: A karkashin wannan bangare yace dole ne akare sirrin dan kasa a gidajensu, wasiku, da maganganu da aka yi ta hanyar wayoyin tarho da sauransu.
Yancin bayyanawa da yada addini: Anan an ce “dan kasa zai iya bayyana addininsa ko kira ya zuwa nasa addinin da kuma canzawa”.

Yancin bayyana albarkacin baki, Yancin yin taron jama’a, Yancin tafiya ciki kasa da kuma zama a duk inda mutum ke so.Yancin Mallaka: na dukiya da kaddarori a duk fadin kasa.

A takaice wandannan wasu ne daga cikin hakkokin ko yanci da kudin tsarin mulki ya bawa yan kasa. Babu shakka wadannan tanade-tanaden an samar da sune don dan kasa ya rayu rayuwa mai kyu, ta yanda zai iya dogara da kansa, hadi da bada gudanarwa wajen ciyar da kasa gaba.

To abin tambayar anan shine shin yan kasa na samun hakkokinsu da kundin tsarin mulki ya yi masu tanadi ? Nasan amsar da kowanenmu zai bayar ita ce a’ah! To me hakan ke nufi ? Karara ya nuna yanda shugabanni ko jagororin kasa suke karya wadancan tanadi da aka warewa yan kasa. A bayyane yake jagorori suna yin karan tsaye da dokokin kasa, ta yanda ya zama abin mulkar ba su da wani yanci sai abinda jagori suke so a tafikar.

Babu shakka abin mulka na da laifin wajen taka doka da su ke yi. Amma abin tambayar me yasa yan kasarnan sukai kaurin suna wajen karya doka ? Amsa: Suna koyi ne da jagorori. Don kuwa da jagorori sun bi doka sun samar da kyakkyawar rayuwa garesu, sun basu duk yancin da zai taimaka su samu hanyar gina kansu zai wahala ka samesu suna aikata mugayen laifika. Amma an bari wasu na ta kashesu, suna fama da yunwa, basu da ikon su aje sai an sace, in sun fadi albarkacin baki a kama su!

Don Allah ya ake so wanda ake mulka ya yi? Maganar gaskiya mafi yawa dole ce tasa su ke fadawa cikin muggan laifuka.

Kamar yanda taken wannan rubutu ya ke DAGA NA GABA ake gane zurfin ruwa. Dan haka mafita daya ce, jagorori da masu mulki su bi doka kafin su iya yaki da masu karya doka a kasa.

Zaku iya aiko mana da naku ra’ayin a adireshinmu: submit@dabofm.com

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00