Labarai

Gwamnatin tarayya ta janye dokar hana tafiye-tafiya, ta amince da bude makarantu

Gwamnatin tarayya ta dage dokar hana zirga zirga ta tsakanin jihohi, tare da amincewa da bude makarantun karama da babbar sakandare.

DABO FM ta tattara cewa wannan na zuwa ne bayan shugaban hadin gwiwar yaki da cutar Kwabid19 na kasa kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya gana da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari sunyi wata ganawa a ranar Litinin.

Boss Mustapha ya bayyana cewa “Ina mai sanar daku cewa shugaban kasa ya karbi rahoto na 5 daga hannun kwamitin yaki da cutar Kwabid19 ta kasa, ya kuma yi duba na tsanake, inda a cikin kashi na 2 na dage dokar kulle ya bayyana dage kulle na sati 4 nan gaba daga Talata 30 ga Yuni zuwa tsakar daren 27 ga Yuli.”

Daga karshe dai kwamitin yaja hankalin jama’a da suci gaba da bin ka’idoji da gwamnati tare da masana kiwon lafiya suka gindaya.

Karin Labarai

UA-131299779-2