#Op-ed: Arewa da munafurcin ‘ya’yanta, Daga Muhammad Dangalan

dakikun karantawa
Dangalan Muhammad (File Photo)

Arewa, yankinmu da ba shi da tamka.

Ana ta kira a zama tsintsiya madaurinki daya, sai dai tsintsiyar arewa ba ta dauruwa a hanyar alkhairi. Ba ma nuna kanmu yana hade sai wani dan cikinmu ya je wani yanki ya aikata musu laifi, a nan ne ya za mu rika tada jijiyoyin wuya muna cewa an yi masa sharri, wasu ma cewa suke yi saboda dan arewa ne Musulmi shi yasa ake masa haka.

Muna kallo masu madafun iko suna kashe mana yanki, muna ji muna gani an mayar da mu tamkar yankin gwada wa aga ran dan Adam daya ne ko sama da haka, matsal-tsalun fyade tsakanin iyaye maza da ‘ya’yansu kanana da sauran manyan abubuwan da suke damunmu.

Daga cikin abubuwan da na lissafa a sama, kama daga kan kafofin yada labarai zuwa kan mutanenmu da suke da tasiri a kafofin yada labarai da sada zumunta, duk wanda ya cika yin magana a kan matsalolin, gani ake yi kamar yana murna da ta’asar da take faruwa. Duk da kasancewar Jaridar Daily Trust a matsayin jaridar da ta kan share hawayen ‘yan Arewa, ita ma ba ta tsira daga zage-zage da furucin batanci a kanta daga ‘yan Arewa ba. Wataran kuma dan rashin ta ido ace sun yi shiru a kan abubuwan da suke damunmu.

A sashi guda, akwai wadanda suke da karfin fada a ji a kafafen sada zumunta ko kuma maganarsu ke da tasiri idan suka furta, su kan yi shiru kan matsalolin Arewa, amma da zarar al’ummar kudu sun taso abu a gaba, nan da nan za su taya su har a kai ga ci.

Wannan munafurcin ina zai kai mu? Halaka!

A makon nan da al’ummar kudancin Najeriya suka dauki azamar nuna borensu ga ayyukan muguntar jami’an SARS, kuma dukkanin alamu sun nuna borensu zai haifar da ‘da mai ido domin kuwa har shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugaban ‘Yan sanda a kan yi wa jami’an garanbawul. A rashin da ido na wasu mutanen arewa, ka ɗa baki suke yi su ce “Ina ruwanmu da muguntar SARS?, ai mu basa yi mana a yankinmu.” Wasu ma cewa suke yi ai mutanen kudun ‘yan danfara ne shiyasa suke koka wa kan kisan da ‘yan sandan suke yi.

A birnin Kano da ranar Allah, ana ji ana gani jami’in dan sanda ya harbe wani matashi mai suna Mus’ab Sammani dan shekara 22 a kan hanyarshi ta zuwa kasuwancinsa da yake yi, kamar yadda BBC ta rawaito. Haka zalika rahotanni sun nuna yadda ‘yan sanda suka harbe wani matashin a kasuwar Waya ta Farm Center dake Kano. Ko maganar ba ka ji.

Duk mun gaza yin komai a kai. Wani abin takaicin yanzu diyar shugaba Muhammadu Buhari, Zahra, ta shiga sahun masu zanga-zangar bore ga irin wadannan kashe-kashe na ‘yan sanda duk da cewa a jiharta ta Katsina an kashe mutane sama da 150 sakamakon ta’addancin ‘yan binduga.

Yaushe za mu farka mu san ciwon kanmu tare da yin kuka idan abu ya same mu?

A arewar da tsoho zai yi wa yarinya fyade iyayenta suce a bar maganar don kar a bata musu sunan ‘ya har ma ya kai su ga barin unguwar da suke zama. A arewar da Uba zai yi wa ‘yarsa fyade, mai unguwa ya nema masa shaidar hauka daga asibiti. A arewar da ake yi wa mai neman hakkinsa kallon mara kishin addini. A arewar da aka dena martaba aure ta hanyar saki a kan lefin da bai wuce sa siga da yawa a shafi ba.

A arewar da babu wanda bai wuce a zage shi ba, lallai har yanzu ba mu shirya farkawa ba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog