Gwamnoni Ne Babbar Matsar Arewa Inji Daitu

dakikun karantawa

Tun bayan dawowa mulkin Siyasa a 1999 kudin tsarin Mulkin ƙasar mu ya bawa Gwamnoni cikakken iko da Mallaka. Inda kaso 90 na Arzikin ƙasa mallakar sune musamman Filayen noma da dazuzzuka, inda ake gino ma’adanai.

Gwamnonin suna karban Rabon arzikin ƙasa daga Gwamnatin Tarayya a kowacce wata, suna tattara haraja daga jihohin su.

Gwamnonin sun tabbatar sun rusa makomar Ƙananan Hukumomi inda sukafi kusa da talakawa, inda basu barin su su sarrafa dukiyar Ƙananan hukumomin domin talaka ya sami sauƙi, kamar yadda doka ta tanaza.

Gwamnatin Lardi da akayi ƙarƙashin Jagorancin Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello ta tsaya tsayin daka gurin tono arzinƙin ƙasa da noma da kiwo da Allah ya azirta Arewa dashi, inda suka tsaya tsayin daka aka gina masana’antu, makarantu, da samarwa Al’umma ayyukan ƴi domin kaucewa zaman banza.

Amma a yau Gwamnonin Arewa sun kasa tsayawa sutabbatar sun yaƙi muguwar Talauci data da baibaye Arewa.

Duk matsalolin dake damun Arewa idan aka tabbatar da wanzuwar Tattalin arziƙi, Arewa zata zama zakara kuma zata zauna daidai.
Matiƙar ba’a yaƙi Talauci ba to akwai barazanar ta’addanci a yankin

Haƙƙin Gwamnoni ne su tabbatar kowani mai Sana’a idan ya fito bashi da fargaba zai iya riƙe kansa da iyalan sa.

Hatta Ilimi bazai ta’ba wanzuwa ba Sai an yaƙi Talauci, mutane basa buƙatar wani Karatu kyauta sabida tsarin Yaudara ne, tsarin babu wata fa’ida ko alfanu daya haifar iyaye dayawa basa iya samun abinci sau 3 a rana tayaya zasu damu da karatun ƴaƴan su.

A kaf faɗin Arewa Babu wata makaranta da zaka nuna ingantacciya wadda Ƴaƴan Talakawa suke karatu acikin ta tare da Ƴaƴa masu iko a Arewa ɗin. Wannan babban naƙasu ne kuma koma baya ne agaremu.

Babbar illa da Gwamnoni Arewa suka ƙara haifarwa yanki dashi shine Masana’antun da Tsohuwar Gwamnatin Arewa tagina sun kasa gyarawa balanta su ƙara gina Sabbi ko akawo masu zuba Jari na cikin gida da ƙetare.

Gwamnonin Arewa haryau sun kasa kawo tsayyen Wutan Lantarki wadda zai raba dubban mutane Da zaman kashe wando.

Gwamnoni Arewa suke da iko da zasu jawo kowa acikin gudanar da ayyuka don cigaban Arewa, amma basa sauraran kowa kuma basaganin ƙima, da Daraja na mutanan da suke faɗa masu gaskiya don su gyara kura kuran su.

Gwamnonin Arewa suna Kallo.
Bankin Arewa.
Kamfanin Masaƙu
Cibiyar cinki da masana’antu ta kano
Jaridar Gaskiya tafi Kwabo
New Nigeria
Maɗabbaƙar buga littafai na Arewa (NNPC) da sauran su suka bari suka mutu. Wannan gurare zasu raba dubban mutane da zaman kashe wando, suka bar su a wulƙance.

Munada Gwamnoni 19 amma abin baƙinciki da takaici haryanzu basu iya gyara abubuwa da Su Sardauna sukayi ba balanta su kawo sabbi wadda zai farfaɗo darajar Arewa.

Kada ku manta kunci moriyar Gwamnatin Arewa, yakamata kutashi tsaye ku fafaɗo da yankin, bamu da inda zamu rayuwa sai nan Ƴan Ta’adda sun Addabe mu, An karya mana Tattalin Arziƙin mu, Sana’o’in na Noma Da kiwo sakamankon ayyukan Ta’addanci. Kunada dama da zaku gina Yankin mu.

Muna kira da ƙungiyar Gwamnonin Arewa data kafa hukuma da zata kula da cigaban Ɗan Adam (HUMAN CAPITAL DEVOLPMENT.

Don farfafaɗo da cigaban yankin.

Kar mu yaudari kan mu Gwamnati Abuja batamu take ba don ba abinda zatayiwa Arewa. Haƙƙin mune mu tashi mu yaƙi abinda ke ci mana tuwo a ƙwarya.

Ƙungiyoyi da ake kafawa da sunan Arewa bazasu irgu ba, amma duka ƙungiyoyin basu da wata manufa da suka cinma wadda, ya sauya makomar Arewa, wajibi ne ƙungiyoyin Arewa Tundaga Kan ƙungiyar Dattawa, zuwa na Matasa su sauya akoma guri guda a tattauna matsaya kuma a ɗabbaka abinda aka tsara, kuma atshi tsaye don aga an sami Nasara.

Sarakuna da Malamai suma jigone da sukeda cikakken ikonda zasu tsawatar, kugujewa Ruɗin Ƴan Siyasa sabida kune Amanar Al’umma ke hannun ku na Jagoranci, Sabida kune Iyayen ƙasa da zaku kira kowa, kuyi masa faɗa don yayi abinda ya dace.

Ƴan Majalissu kuma kunada taku babbar baraka da kuke kawo mana, sabida ƙudurorin da kuke kaiwa a Majalissa basu kawo mana Alfanu. Yakamata ku dunga tsayawa kuna bawa Al’umma da kuke wakilta dama don su faɗi matsalar su, sai kuntabbatar kun kai ƙudiri majalissa da yawun Talakawa.
Kuɗaɗen mazabu suma bakwa kashe su bisa yadda doka ta tanaza wannan shima babbar koma baya ne Agaremu.

Allah ya bamu ikon Gyarawara.

Comr Sani Musa Daitu
Ɗan Rajin kare haƙƙin Ɗan Adam
(Human Rights Activist)
Edida na Jaridar Amana
Giwa Jihar Kaduna
08035880730
[email protected]

Karin Labarai

Sabbi daga Blog