Labarai

Ajimobi yayi daga-daga da Naira biliyan 5 mako 3 kafin ya mika mulki ga sabon gwamna

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya zargi tsohon gwamnan jihar Abiola Ajimobi da kwashe makudan kudade daga cikin asusun jihar.

Gwamnan ya zargi Ajimobi da yin sama da naira biliyan biyar (N5b), yayin da ya rage saura makonni uku ya mika kujerarshi.

Gwamnan ya bayyana hakane a lokacin da yake hira da manema labarai akan abubuwan da suka shafi gwamnatin jihar.

Ya ce: “A ranar 6 ga watan Mayu, 2019, inda ya rage saura makonni uku na hau kujerar, tsohuwar gwamnatin jihar nan ta cire naira biliyan biyar da digo biyu (N5.2b), inda ta bar naira dubu sha tara (N19,000) kacal a cikin asusu a ranar 29 ga watan Mayu.

“Dole wadanda suke da hannu akan bacewar wannan kudin suyi bayani akan yadda suka kashe wadannan kudaden ga al’ummar jihar nan.”

Inda ya kara da cewa ya bar bashin fiye da Naira biliyan 150.

UA-131299779-2