Labarai

Masana a Amurka sun gano yin azumi sau 2 a mako na kara tsawon rai da riga-kafin cututtuka

Malaman Kimiyyar Amurka sun bayyana cewar sakamakon wani bincike da suka gudanar ya bayyana yin azumi a kowanne mako ko kuma kame baki daga barin cin abinci na wasu awanni a rana na kara tsawon rayuwa tare da riga-kafin cututtuka da dama.

Sakamakon binciken da aka buga a mujallar Likitanci ta New England ya ce cin abinci a cikin awanni 6 zuwa 8 sannan a kame a awanni 16 zuwa 18 na kowacce rana na kara tsawon rai, rage karfin harbawar jini da riga-lafin cututtuka da dama.

Rahoton mu na Dabo FM wanda muka samu daga jaridar TRT ya ce yin azumi a kwanaki 2 a kowanne mako na iya maganin cututtukan zuciya, kiba da ciwon sukari a saboda haka ake shawartar mutane da su yi hakan.

Binciken da aka gudanar a kan mutane da dabbobi ya nuna yin azumin na daidaita yanayin sarrafuwar abinci da gudanar jini a jikin dan adam, sannan yana sabunta lafiya.

Haka zalika na magance kwayoyin Insulin na jikin mutum wanda hakan abu ne mai kyau ga masu ciwon sukari. 

Karin Labarai

Masu Alaka

Gobe Litini, za’a tashi da azumin Ramadana a kasar Saudi Arabia

Dabo Online

Yadda za mu kare kan mu daga kamuwa da cutar zazzabin ‘Lassa’ -Dr Abdul’aziz T. Bako

Muhammad Isma’il Makama

Anga jinjirin watan Shawwal a Damaturu, Talata 1 ga Shawwal

Dabo Online

Sojojin Amurka 34 sun sami tabin kwakwalwa bayan harin da Iran ta kai musu

Muhammad Isma’il Makama

Za a tsige shugaba Donald Trump

Rilwanu A. Shehu

Yanzu-Yanzu: Mahaifin matashin da baturiya ta biyo Kano zai kai maganar gaban jami’an tsaro na ‘SSS’

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2