0
Alhaji Shehu Shagari, tsohon shugaban Najeriya, ya cika shekara daya da rasuwa.
DABO FM ta tattaro cewa tsohon shugaban ya rasu a ranar 28 ga watan Disambar shekarar 2018 a garin Abuja bayan fama da rashin lafiya.
Ya rasu yana da shekara 93 a duniya, ya bar ‘ya’ya 19, Maza 8 da Mata 11.
Kafin rasuwarshi ya kasance shugaban Najeriya daga shekarar 1979 zuwa 1983 lokacin da shugaba Muhammadu Buhari yayi masa juyin mulki.
Yayi Minista a zamanin shugaba Sir Abubakar Tafawa Balewa daga shekarar 1960 zuwa 1966.
Ya kasance daga cikin manyan ‘yan Majalissar kolin Musulunci a fadar Sultan wanda ya rike mukamin Turakin Sakkwato tin daga shekarar 1962.
