Budurwa ta guntule wa kawarta dan yatsa bisa dalilin kiranta da ‘Banza’ a garin Kaduna

Karatun minti 1

An gurfanar da Zainab Muhammad a kotun dake Magajin Gari bisa tuhumar ta da guntule wa kawarta dan yatsa tare da zubar mata da hakora, hadi da kiranta da sunan banza.

Mai shari’a Murtala Nasir ne ya jagorancin shari’ar inda ya bada bailin Zainab tare da umartar ta gabatar da shaidar da zai biya N70,000 a kotu.
Sashin Hausa na Jaridar Premium Times ta bayyana cewa; mai shari’a Nasir ya dage zaman kotun har zuwa 23 ga watan Julin 2019 domin wacce aka ciza ta samu lafiya.

Haza zalika Premium Times Hausa ta rawaito cewa; “Yayin da kotun ta zauna lauyen da ya shigar da karar Aliyu Ibrahim ya bayyana cewa Jummai Babangida dake zama a Titin ‘Katsina Road’ ce ta kawo karar a ofishin ‘yan sanda dake Magajin Gari bayan abin ya faru.

Ibrahim yace Jummai ta bayyana wa ‘yan sanda cewa haka kawai a ranar 7 ga watan Yuli da karfe takwas na safe Zainab wacce ‘yar kasuwa ce ta gamu da ita a hanya ta kawai sai ta hauta da duka acikin haka ne fa ta kama hannayenta ta guntule da cizo.

“Jummai ta ce Zainab ta kira ta maiya, ta ji mata rauni a jiki sannan ta yi mata kashejin cewa daga ranan kada ta yadda su yi ido hudu kuma, domin duk inda suka hadu sai ta sake narkarta.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog