‘Yan bindiga sun harbe kawun Sanatan daya daddaki wata mata dake shayarwa

dakikun karantawa

Sashin Hausa na Legit.ng ya rawaito cewa; “Yan bindiga sun harbe kawun sanata Elisha Abbo, sanatan da aka gani a wani bidiyo ya na dukan wata mata a shagon siyar da kayan jima’i na robobi.

Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da goggon sanata Abbo da ke shayarwa a harin da suka kai yau Asabar 13 ga watan Yuli 2019 a jihar Adamawa.

Hukumar yan sanda da jama’ar garin sun bayyana cewa an kai harin a Muchalla dake a karamar hukumar Mubi ta arewa dake a jihar Adamawa.

Yan uwa da abokan arzikin goggon sanata Abbo sun bayyana cewa ta haihu kimanin kwanaki 11 da suka wuce.

Mutanen garin sun bayyana ma jaridar Premium Times ta wayar salula da misalin karfe 1:00 na rana, inda wani mutum da abin ya faru akan idonshi ya bayyana cewa bayan da yan bindigan suka shigo gari sai suka “Tunkari gidan iyalan sanata Abbo kai tsaye inda suka dauke goggonshi dake shayarwa. Ta haihu kimanin kwana 11 da suka wuce.”

“A lokacin da suke kokarin tserewa, kawun Abbo ya fito daga cikin dakinshi, bayan da ya gansu sai yayi kokarin sanar da jama’a. Nan take yan bindigar suka bude mashi wuta wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarshi su kuma suka tsere. A yanzu haka ana ta jimami a kauyen.”

Mai magana da yawun rundunar yan sanda na jihar Adamawa, Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da afkuwar lamarin. Ya bayyana cewa an tura yan sanda su bi sawun yan ta’addan.

Ya bayyana cewa “An tura yan sanda na musamman na babban sifeton yan sanda tare da yan sanda masu yaki da garkuwa da mutane da bangaren kisa don su ceto wadda aka yi garkuwa da ita su kuma kama yan ta’addan.”

Legit.ng

Karin Labarai

Sabbi daga Blog