(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Canada ta roki shugaba Buhari ya tura ‘Yan Najeriya miliyan 1 zuwa kasar

dakikun karantawa

Firaministan kasar Canada, Justin Trudeau, ya roki shugaba Muhammadu Buhari ya kyale ‘yan Najeriya miliyan 1 su shiga kasar Canada karkashin shirinta na “Ayyuka da aka tsara don baki.”

Gidan Talbiji na CBTV ya rawaito cewa ‘yan Najeriya na daga cikin mazauna kasar Canada wadanda ke taimakawa kasar wajen habbaka tattalin arzikin ta.

Firaministan yace:

“Bazamu iya kauda kai daga gudunmawar da baki suke bamu ba musamman ‘yan uwanmu maza da mata ‘yan Najeriya.”

Firaministan ya kara da cewa a shekaru uku da suka wuce, kasar ta baiwa dukkanin ‘yan Najeriya mazauna kasar shedar zama ta dun-dundin har wadanda suke zaune ba bisa ka’ida ba.

“Duk mun basu shaidar zama, kuma muna fatan kowa zai nemi izinin zama dan kasar. Yana da kyau musan adadin duk wanda yake zaune da kuma wadanda muke so mu kara dauka.”

A wata wasika da ya aikewa Ofishin jakadancin Najeriya a kasar ta Canada, yace tsarin ya kunshi baiwa dukkan wadanda suke son zama a kasar Canada aikin yi tin kafin saukar su kasar.

“A mako mai zuwa za’a bude shafin yanar gizo-gizon da ‘yan Najeriyar zasu iya cikewa, yanzu haka mun tanadi aiyuka miliyan 6 kuma muna fata shugaba Buhari zai bar ko da mutane miliyan 1 ne.” – Cewar Mr Shadrack Scott, mai magana da yawun hukumar samar da aikin yi ta kasar Canada.

Tin a farkon shekarar 2019, kasar Canada ta bayyana shirin ta na neman mazauna a kasar.

Inda a shekarar 2017 kasar ta karbi bakuncin kusan mutane 350,000, ta kuma bayyana tana da shirin karbar yan gudun hijira miliyan 1 a bana.

Kasar tace habbakuwar tattalin arzikinta ya samo asali ne bisa shigowar baki dayawa kasar.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog