(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Daliban jami’ar Al Qalam Katsina sun bani kunya wallahi – Mufti Menk

Karatun minti 1

Fitacce daga cikin Malaman addinin Islama a fadin duniya, Mufti Menk Isma’il a bayyana cewa daliban jami’ar Alqalam dake jihar Katsina sun bashi kunya.

Mufti Menk yayi wannan jawabi ne a daren ranar Lahadi, bayan da aka gayyace makarantar domin bada karanta da nasiyoyi a jami’ar kamar yacce ya saba.

DABO FM ta binciko Menk yayi kalamin nuna rashin dadi ne biyo bayan dabi’ar daliban da yace ta bashi mamaki yacce suka rika surutu a dai dai lokacin da ake gudanar da karatu.

“Wallahi baku kare mutuncin kanku ba, Ina matsayin uba a wajenku, kuma zan fada muku gaskiya.”

“Gaskiya itace kun yin surutun daya wuce tunani daga bakunan ku. Surutun kun ya bani kunya sosai.”

“Dan haka yanzu zan tafi, wataran zamu saka haduma idan Allah ya nufa, Allah Yayi muku albarka baki daya.”

Bayan tattaunawa da wakilin mu yayi da wasu daliban makarantar, sun bayyanawa DABO FM cewa, Sheikh Mufti ya fara karatun ne surutun dalibai yayi yawa, har ranshi ya baci, lamarin daya sa bai karasa ba ya gintse karatun.

Kalli Bidiyo

Karin Labarai

Sabbi daga Blog