Labarai

Kowanne ‘dan Najeriya yana da cikakken ‘yanci a duk jihar da yake zama – Sarki Sunusi

Mai martaba sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sunusi II, ya bayyana cewa kowanne dan Najeriya yana da ‘yanci kamar kowa a duk garin da yake zama.

Mai martaba Sarki ya bayyana haka ne a wajen taron bikin cikar shekaru goma da nadin Sarkin kabilar Igbo a jihar Kano.

Mallam Muhammadu Sunusi II, yayi maganar ne bisa nuna rashin goyon bayanshi da wata sabuwar doka da ake kafawa a wasu sassan Najeriya na nuna wasu a matsayin bakin haure zuwa wata jihar.

Sarkin dai ya bukaci ‘yan Najeriya da yiwa junansu da’a a dukkanin jihar da suke zama ba tare da nuna bambancin yare, addini ko al’ada ba.

Sarkin ya bayyana mutanen Kano a matsayin mutanen da basu da kyashi ko nunawa wasu banbancin yare ko addini.

“A Kano, bamu san da batun yan jiha na asali da wadanda ba yan asalin jihar ba. An gina wannan birnin ne kuma arzikinta da ingancinta sun kasance akan budaddiyar yanayinta da masaukinta.” – Sarki Sunusi. via Hausa Legit.ng

Daga karshe ya bukaci al’ummar kabilar Igbo da su cigaba da tabbatar da zaman lafiya da sauran ‘yan Najeriya a Kano.

“Mu yan Najeriya ne, mu kuma mun kasance yan adam masu fuskantar kalubale iri guda.

Karin Labarai

Masu Alaka

Sarkin Kano, Sunusi II ya mayarwa da Ganduje martani a karon farko

Dabo Online

Malamai miliyan 1 na kasar Kanada sun nada Sarkin Kano shugaban kwamitin ‘Mashawarta’

Dabo Online

Sarkin Kano Sunusi II ya zama shugaban jami’ar gwamnatin jihar Ekiti

Dabo Online

Hawaye sun zubo daga Idon Sarki Sunusi yayin nuna alhinin mutuwar Jariri akan N1500

Dabo Online

To fa: Sanusi ya nemi Osinbajo yayi masa mataimakin shugaban kasa lokacin da Buhari bashi da lafiya

Muhammad Isma’il Makama

Sarkin Kano, Muhammad Sunusi II ya dawo Najeriya bayan shafe kwanaki a Birtaniya

Dabo Online
UA-131299779-2