Tsohuwar Minista, Amina Muhammad tayi kira da adena kyamatar ‘Yan Madugo da Luwadi a duniya

dakikun karantawa

Mataimakiyar babban sakataren majalissar dinkin duniya, Haj Amina Muhammad, ta nuna goyon bayanta ga auren jinsi.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, Majalissar dinkin duniya ta UN da sauran kungiyoyin kare hakkin bin adama sunyi kira cewa lokaci yayi da yakamat a dena kyamar duk masu yin madigo da luwadi a kasashen duniya baki daya.

Majalissar a shekarar 2015, tayi kira ga jami’anta na sassan duniya dama wasu hukumomi da suyi kokari wajen baiwa ‘yan madigo da luwadi kariya daga tsangwama da tsana a duk inda suke.

Haka zalika Jaridar dai ta rawaito cewa, kasashe dayawa sunki bin shawarar majalissar dinkin duniyar akan batun ‘yan madugon da Luwadi.

Wasu kasashen kuma sun aminta da shirin tare da basu kariya a matsayin girmamawa ga hakkinsu na ‘dan adam.

DABO FM ta binciko shafin tsohuwar minister a Najeriya, Ms Amina J Muhammad, ‘yar asalin mutanen arewar Najeriya da akafi sani da riko da addinin musulunci a Najeriya, ta bayyana goyon bayanta ga baiwa ‘yan luwadi da madigo damar yin duk abinda suke so a kowacce kasa.

Ta bayyana cewa yakamata a rika girmama ‘yan madigo da luwadi saboda hakki da suke dashi a matsayinsu na ‘yan adam, suna da damar suyi duk abinda suke so.

Amina Muhammad ta wallafa sakon ne a shafin na twitter.

“Mu tashi don ganin baiwa duk wani dan adam hakkinshi, kowa yana da hakki ya mora da samun daraja. #Alfahari da 🌈

Karin Labarai

Sabbi daga Blog