Ganduje ya kori motar da aka ciko da ‘yan cirani zuwa Kano daga Abuja

Karatun minti 1

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje yayi nasarar kame wata mota kirar Gingimari da aka ciko da mutane zuwa jihar Kano.

Ranar Juma’a da ta gabata dokar hana shiga da fita daga jihar Kano ta fara aiki a yunkurin gwamnatin Kano na hana yaduwar Coronavirus.

Biyo bayan rahotanni da aka samu na cewar duk da umarnin hana shigowa Kano, ana zargi jami’an tsaro da karbar cin hanci a kan iyakokin jihar domin bari a cigaba da shiga jihar.

DABO FM ta tattara cewar; A yau Litinin gwamna Ganduje ya kai sumame kan iyakar shigowa jihar Kano ta titin Zaria, inda ya samu nasarar kama wata mota cike da mutane da aka shigo dasu jihar.

Motar ta taso ne daga garin Madalla dake tarayyar Abuja, kamar yadda mataimakin gwamnan a harkokin labarai ya bayyana.

Ya kuma ce tini dai gwamnan ya umarci mitar da mutanen su koma inda suka fito.

Karin Labarai

Latest from Blog