Labarai Tattaunawa

Covid-19: Matakan da gwamnatin Kaduna ta dauka shi ne mafita – Dakta Hussaina Adamu

A dai-dai lokacin da gwamnatoci a kowanne mataki suka dukafa wurin yaki da cuta mai sarke numfashi wato COVIC19, an yaba da matakin da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka na wadata asibitoci da magunguna da sauran kayayyakin da suka dace domin kawar da cutar a sassan Jihar.

Shugabar Asibitin gwamnati na Gambo Sawaba da ke Kofar Gayan Zariya Dakta Hussaina Adamu ta bayyana hakan sa’ilin zantawarta da Dabo FM a ofishin ta.

Ta ce, matakin da ake a halin yanzu game da cutar ta COVIC19, babu matakin da ya kamata a dauka illa wanda ake kai yanzu na takaita zirga-zirgan ababen hawa da na al’umma saboda kare lafiya da ma dukiyoyin su.

A cewar ta, ya zama wajibi al’umma su dauki dabi’ar takaita shiga Jama’a barkatai, da yawan taruka saboda yadda cutar ke yaduwa ta fuskoki da dama.

“Kadan daga cikin alamomin cutar sun hada da zazzabi mai zafi da tari da atishawa da kuma daukewar numfashi”, a cewar Dakta Adamu.

Ta kara da cewa, sam bai kamata mutanen da ke garuruwan da wannan iftila’in ta afka masu su rika fita ba, kuma wanda suke waje bai kamata su rika shiga ba.

Ta shawarci wanda suka dawo daga tafiye-tafiye daga sassa daban-daban su killace kansu na tsawon akallla kwanki 14, domin gudun ko suna dauke da nau’in wannan cuta.

Dr Hussaina, ta bukaci iyaye su rika Kula da kaiwa da komawar yaran su a irin wannan lokaci har ma da sanin abubuwan da za su yi mu’amala da shi na cimaka ko na sha.

Daga karshe Dr Hussaina, ta yi addu’an samun sauki ga gwamna Malam Nasiru El-rufa’i da kuma sauran al’ummomi da suka kamu da wannan cuta.

Karin Labarai

Masu Alaka

Da dumi-dum: Gwamna Zulum ya kulle iyakokin jihar Borno

Dabo Online

Alkaluman ‘Corona Virus’ ya zama 30 bayan sake tabbatar da 3 a yammacin Lahadi

Dangalan Muhammad Aliyu

Gwamnati ba zata tallafawa wadanda suke da sama da N5000 a asusun banki ba – Sadiya Faruk

Dabo Online

Yanzu yanzu: An samu karin mutum 4 masu dauke da Coronavirus, jumilla 135 a Najeriya

Dangalan Muhammad Aliyu

Buhari ya bada umarnin rabar da Shinkafar da Kwastam suka kama

Dabo Online

Yanzu yanzu: Alkaluman ‘Corona Virus’ sun zama 40 bayan sake tabbatar da 4 a daren Litinin

Faiza
UA-131299779-2