Labarai

Kwanaki 30 cif da dauke Abubakar Idris Dadiyata ‘Babu gaira babu dalili’

Yau ranar Talata, 3 ga watan Satumbar shekarar 2019, aka kwana 30 da dauke matashi Abubakar Idris Dadiyata.

Tin a ranar 3 ga watan Agustar 2019, wasu mutane da ba’a san ko suwaye ba, sukaje har gidan matashi dake jihar Kaduna suka daukeshi, lamarin da yayi sanadiyyar har zuwa yanzu babu labarinshi.

Hukumar DSS da aka zarga tin farkon dauke matashi, ta bayyana cewa bata tsare da matashin, hasalima bata tura jami’anta unguwar su Abu Dadiyata aiki a wannan dare ba.

Dadiyata, malami a jami’ar Katsina ya kasance dan gwagwarmaya da fafutukar neman gwamnatin APC a Najeriya da jihar Kano su yiwa dukkanin mutanen da suke jagoranta adalci.

Abubakar Idris, wanda akafi sani da Abu Hanifa Dadiyata, dan Jami’iyyar PDP, mai bin tsari da darikar Kwankwasiyya, tsagin da akeyin ‘Kare-Jini, Biri-Jini’ tsakaninsu da bangaren gwamnatin jihar Kano na Gandujiyya.

Manyan mutane a Najeriya sunyi Allah-Wadai da kamun matashin, hukumomin kare hakkin dan Adam na duniya sun biye musu sahu wajen kiran wadanda suke tsare da shi su sake shi.

Jagora a jami’iyyar APC, Alhaji Buba Galadima, ya zargi wani gwamnan Arewa wanda bai fadi sunanshi ba a matsayin wanda yake da hannu wajen tsare maatashin.

Karin Labarai

UA-131299779-2