Koren shayi yana kara kaifin basira – Masana Lafiya

Masana kiwon lafiya na Jami’ar Basel dake kasar Swizalan sun binciko cewa shan koren shayi yana kara kaifi da karfin basira.

Masanan sun kara da cewa Shan Koren Shayi yana aiki a jikin mutum tamkar tsafi wajen aiwatar da ayyukan da yakeyi a jikin dan Adam.

Jami’ar ta tabbatar da amfanin Koren Shayin wajen rage kiba, rage gajiya, tare da tsayar da kwayoyin dake karfafa girman Cancer a jikin dan Adam.

A shekarar 2014, Mujallar Psychopharmaclogy ta wallafa binciken inda ta tabbatar da Shan Shayi yana inganta kyakkawar mahada da bangaren “Frontal Lobe” dake jikin kwakwalwa.

Dadin dadawa kuma; Yana inganta aikin Parietal Lobes wanda yake karfafar Iyawar sassan kwakwalwar wajen iya tuna wani abu yake kuma hana mantuwa.

Masu Alaƙa  Zogale yafi kaza: Najeriya zata shuka zogalen naira Biliyan 9

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.