Mun dauki niyyar fitar da ‘Yan Najeriya miliyan 100 daga bakin Talauci a shekaru 10 masu zuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinshi tayi niyyar fitar da ‘Yan Najeriya miliyan 100 daga bakin Talaucin da yayi musu katutu a cikin shekaru 10.

DABO FM ta cewa shugaba Buhari ya bayyana haka ne a jawabin kaddamar da shirin rantsar da sabbin Ministocin da zasuyi aiki tare dashi. Taron da aka gudanar a ranar Litinin, 19 ga watan Agustar 2019.

A yayin taron da aka gudanar da cikin fadar gwamnatin dake birnin Abuja, shugaban yayi kira ga sabbin Ministoci da suyi aiki tukuru a matsayin tsintsiya mai madauri daya wajen kawo cigaba a kasa baki daya.

Da yake jawabi, shugaba Buhari ya bayyana musu cewa; gwamnati dama al’ummar Najeriya zasu dogara dasu wajen fito musu da ayyukan alheri musamman wadanda zasu fitar dasu daga kangin Talauci.

Buharin yace; “Na dora yarda ta akanku.”

Masu Alaƙa  Buhari ya dawo Najeriya bayan shafe kwanaki 10 a kasar Birtaniya

Shugaba Buhari yayi kira ga Ministoci da su hada hannu wajen taimakawa juna domin yin aiki tukuru.

“Dole ne muyi aiki a tare, mu zama kamar kungiya. Aiki tamkar tsintsiya mai madauri daya yana bukatar kowa ya san abinda wani yakeyi. Dole ne ku zamana kuna tattaunawa a junanku, rashin tattaunawa yana kawo nakaso wajen tafiyar ayyuka.

“Muna aiki ne domin fitar da Najeriya daga kangin Talauci tare da dora su a hanyar samun dace. Mun daura niyyar fitar da ‘Yan Najeriya miliyan 100 daga kuncin Talauci nan da shekaru 10 masu zuwa.

Daga karshe ya taya dukkanin Ministocin murna.

“Ina taya sabbin zuwa, wadanda zasu hadu da wadanda daman suna nan murna. An baku mukamin ne domin ku bawa shugaban kasa Shawara wajen tafiyar da harkokin Najeriya.

“Babbar dama ce na yiwa kasa aiki, don haka dole ku karbi damar da hannu bibbiyu wajen yin dukkanin kokarinku.

Masu Alaƙa  Zamu fitar da 'yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci - Buhari

Bayan Mataimakin shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha sun gama jawabansu ne aka shiga ganawar sirri tsakanin gwamnatin da Sabbin Ministcocin da zaa rantsar a ranar Laraba.Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: