Labarai

Na dora yarda ta gareku – Buhari ya fadawa sabbin Ministoci

A ranar Laraba ne shugaba Muhammadu Buhari zai rantsar da sabbin Ministocin da Majalissar Dattijai ta gama tantancewa bayan daya aike mata da sunayensu.

DABO FM ta binciko cewa; Shugaba Buhari ya kaddamar da fara shirin rantsuwar a yau Litinin, a fadar gwamnatin Najeriya dake birnin Abuja.

Da yake jawabi, shugaba Buhari ya bayyana musu cewa; gwamnati dama al’ummar Najeriya zasu dogara dasu wajen fito musu da ayyukan alheri musamman wadanda zasu fitar dasu daga kangin Talauci.

Buharin yace; “Na dora yarda ta akanku.”

Shugaba Buhari yayi kira ga Ministoci da su hada hannu wajen taimakawa juna domin yin aiki tukuru.

“Dole ne muyi aiki a tare, mu zama kamar kungiya. Aiki tamkar tsintsiya mai madauri daya yana bukatar kowa ya san abinda wani yakeyi. Dole ne ku zamana kuna tattaunawa a junanku, rashin tattaunawa yana kawo nakaso wajen tafiyar ayyuka.

“Muna aiki ne domin fitar da Najeriya daga kangin Talauci tare da dora su a hanyar samun dace. Mun daura niyyar fitar da ‘Yan Najeriya miliyan 100 daga kuncin Talauci nan da shekaru 10 masu zuwa.

Daga karshe ya taya dukkanin Ministocin murna.

“Ina taya sabbin zuwa, wadanda zasu hadu da wadanda daman suna nan murna. An baku mukamin ne domin ku bawa shugaban kasa Shawara wajen tafiyar da harkokin Najeriya.

“Babbar dama ce na yiwa kasa aiki, don haka dole ku karbi damar da hannu bibbiyu wajen yin dukkanin kokarinku.

Bayan Mataimakin shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha sun gama jawabansu ne aka shiga ganawar sirri tsakanin gwamnatin da Sabbin Ministcocin da zaa rantsar a ranar Laraba.

Masu Alaka

Kisan Kolade Johnson abin baƙin ciki ne ƙwarai da gaske – Shugaba Buhari

Dabo Online

Buhari ya kaddamar da kwamitin cigaban yankin Arewa maso Gabashin Najeriya

Dabo Online

Zuwan Buhari Kano: Shin Buhari yana goyon bayan ‘yan rashawa?

Dangalan Muhammad Aliyu

Manyan Najeriya basa kauna ta – Shugaba Buhari

Dabo Online

Zamu fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci – Buhari

Dabo Online

Zaben Gwamna: Shugaba Buhari ya kammala kada kuri’arshi a mazabarshi dake Daura

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2