//

Tarihi: Shin da gaske Sayyadina Umar A.S ya taɓa aika saƙo daular Borno?

dakikun karantawa

[avatar user=”ibrahim” /]

Shin da gaske Sayyadina Umar ya taba aika sako daular Borno?

Wakilin DABO FM a garin Maiduguri, Ibrahim Mustapha yayi mana sharhin wannan tambaya.

Mawallafa Tarihi dadama suntafi akan Eh, amsar wannan tambaya dake sama, shiyasa ma daga sunansu na sarri zakagane cewa kabilar Kanuri sunada dogon tarihi akar kashin addini shi yasa suna da wani suna na sirri wanda da shi suke gane asalin su.

Sunayansu kuwa sune na farko
1.Tara … Sunfitone daga Iraqi
2.Nguma … Sunfitone daga Yaman
3.Maame … Sunfitone daga madina
4.Ngala … Sunfitone daga Habasha
Borno ba ta taba zama a karkashin tutar daular Usmaniya ba.

Daular Borno tsohuwar Daula ce a Afirka da aka kafa tun kafin karni na 10 wacce ta hada da yankunan da yanzu ke cikin Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da Sudan har zuwa Libiya.

Daular Kanem ta El Kanemi ta samo asali ne daga daular Saifuwa.

Masana tarihi sun ce mutanen Saifuwa daga Yemen ne suka fara kafa daular musulunci a Borno, tsawon shekaru 1000 da suka gabata.

Muhammad al-Amin ElKanemi ya kafa Daular Kanem ne a karni na 18, bayan kawar da daular Saifuwa wadanda sarakunanta suka yi mulki shekaru da dama.

Rubucen -rubucen masana tarihi sun nuna cewa Kalmar Borno ta samo asali ne daga kalmomin Larabci, “Bahar Nur”
wato ma’ana kogin haske. Kuma saboda kasancewar Borno gidan Al Qur’ani ne kuma gidan Musulunci ne dalilin ke nan da ya sa sarakunan farko suke kiranta “Bahar Nur”, ma’ana kogin haske na musulunci Daular Borno ta kafu sama da shekaru 1000 Tarihi ya nuna cewa Kanuri da suka kafa Borno daga Yemen suka fito, wato tsatson wani sarki ne da aka yi a Yemen Said Ibn Dhi Yazan da ake kiransa Malik al-Himyari tun kafin zamanin Annabi SAW, wanda ya kafa dauloli a India da Fasha.

Tarihi ya nuna mutanen Ibn Dhi Yazan suna cikin wadanda suka amince su ba sahabban Annabi SAW mafaka bayan hijirarsa daga Makkah zuwa Madinah.

Yemen ne asalin Kanurin da suka kafa mulki a Borno daga daular Saifuwa’ a.
Daular Borno ta yi zamani da Sahabbai, kuma daular ta kafu ne tun kafin zuwan Annabi SAW.

Tarihi ya nuna sarakunan Borno sun aika da wasika suna neman malamai da za su koyar da addini zuwa ga Amr al-As gwamnan Misra, wanda shi kuma ya tura Uqba Ibn Nafi.

Sarakunan Borno sun karbi malamai daga wajen Ibn Nafi a zamanin Sayyadina Umar RA, amma wasu litattafan tarihi sun nuna cewa a zamanin Sayyadina Usman RA ne.

Daular Borno tazauna tare da yankin turawan Birtaniya da Jamus.

Rabeh Zubair Ibn Fadlallah mutum ne da ya taso daga Sudan, wanda ke sana’ar fataucin bayi, inda yake saye ya kuma sayar da bayi.

Masanin tarihi Zanna Boguma ya ce fataucin bayi ne dalilin da ya sa Rabeh ya yaki Borno. A 1893 ne Rabeh ya kawo wa Borno hari.

Rabeh Zubair Ibn Fadlallah ne ya rushe tsohuwar daular Borno bayan ya kaddamar da yaki kuma ya samu galabar kwace iko ya mayar da Dikwa a matsayin babban birnin daularsa.

Rabeh ya kashe sarakunan Borno guda biyu, Shehu Kyarimi da Shehu Sanda Wudoroma.

A 1900 sojojin Faransa na mulkin mallaka suka kashe Rabeh bayan ya yi mulki a shekaru bakwai da watanni bakwai da kwanaki bakwai a Borno. Bayan sun kashe Rabeh ne suka aza Shehu Sanda Kura daga zuriyar Elkanemi a matsayin Shehun Borno a Dikwa a 1900.

Jihadin Shehu Usman Danfodio ya faru ne a 1804, inda ya kafa tutocinsa a daulolin kasashen Hausa a 1805.

Danfodio bai yaki Borno ba saboda Borno ansame ta cikin addinin muslinci da sangayoyin karatun allo.
Daga baya Danfodio da El Kanemi sun dawo sun fahimci juna inda suka amince kuma suka tabbatar da cewa babu abin da ke tsakaninsu illa aminci da yan uwantaka na addinin musulunci.

Borno bata taba zama a karkashin tutar daular Usmaniya ba domin Borno tana da tarihi na musulunci da malamanta sama da shekara 1000 kafin kafuwar daular Usmaniya a Sokoto, shiyasa nadin rawanin masarautar Borno ya banbanta dana yankin yammacin Najeriya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog